1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Rice a Gabas ta tsakiya

November 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvL1

Sakatariyyar harkokin wajen Amurka wato CR ta samu galabar sasanta rikicin dake tsakanin Israela da Palasdinawa a dangane da da batun tsallaka shingen dake akwai a tsakanin juna na yankin Gaza, wanda yayi iyaka da kasar Masar.

CR wacce a yanzu haka ke yankin don gudanar da ziyarar aiki, bayanai sun shaidar da cewa ta dage dawowarta izuwa gida da kwana daya don tabbatar da cewa an cimma matsaya guda game da wannan rikici.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito Rice na fadin cewa, nan da kwanaki goma masu zuwa za a bude wannan shinge don ci gaba da shigi da fici a tsakanin yankin na Palasdinawa da kasar ta Masar a hannu daya kuma da Israela.

Da yawa dai daga cikin Palasdinawa na kallon wannan al´amari a matsayin kafa da zata taimaka wajen shigi da ficin kaya daga yankin na Gaza izuwa ketare.