Ziyarar Recep Tayyib Erdogan a Berlin | Labarai | DW | 09.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Recep Tayyib Erdogan a Berlin

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta karɓi baƙunci Firayim Ministan Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan

default

Recep Tayyib Erdogan ya ziyarci Merkel

A Berlin, babban birnin Tarayyar Jamus shugabar gwamnati, Angela Merkel ta gana da Firayim Ministan Turkiyya Recep Tayyib Erdogan.

Magabatan biyu sun tattauna batutuwa daban-daban, da su ka jiɓanci ma´amila tsakanin Jamus da Turkiyya, hasali ma batun tsaro da kuma siyasa a Turkiyya bayan zaɓen raba gardama, wanda a sakamakonsa aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima a watan Satumba da ya wuce.

A wani taron manema labarai na haɗin-gwiwa, Recep Tayyib Erdogan ya yi kira ga Jamus ta sa baki domin a gaggauta karɓar Turkiyya memba a Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU). Can ma kafin ya fara wannan rangadi, sai da Erdogan ya yi suka ga ƙasashen EU game da tafiyar hawainiyar da su ke yi wajen amincewa da ƙasarsa a matsayin memba.

Ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a a Jamus ta gano cewar kashi kusan 70 cikin ɗari na Jamusawa na adawa da karɓar Turkiya a cikin EU.

A yayin da ya ke tsokaci game da batun shugaban jami´iyar CSU mai ƙawance da CDU ta Angela Merkel ya ce ya kamata gwamnati ta tsaurara matakai game baƙi musamman Turkawa da Larabawa waɗanda ke nuna ɗari-ɗari wajen sajewa da al´adun Jamus.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas