Ziyarar Qurei a Berlin | Siyasa | DW | 17.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Qurei a Berlin

An gudanar da ganawa tsakanin P/M Palasdinawa Ahmad Qurei tare da mashawarciyar shugaban Amurka akan manufofin tsaro Condoleeza Rice da shugaban kasar Jamus Johannes Rau da kuma jami'an gwamnatin kasar

Ahmad Qurei da Condoleeza Rice

Ahmad Qurei da Condoleeza Rice

A hakikanin gaskiya dai, wannan ganawar ba an shirya ta ba ne tun da farko fari. Ita Condoleeza Rice, mashawarciyar shugaban Amurka akan al’amuran tsaro tana kan hanyarta ce ta zuwa Mosko ta kuma yi amfani da wannan dama domin ganawa da P/M Palasdinawa dake ziyarar Jamus yanzu haka. Daga baya-bayan nan Ahmad Qurei’i ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell a saboda haka yana da cikakkiyar masaniya a game da matsayin Amurka a sabanin da ake yi da Isra’ila. Amma duk da haka ganawar a birnin Berlin tana da wani muhimmanci na musamman. Da farko dai ta ba da kafar musayar ra’ayi tare da daya daga cikin gaggan mashawartan shugaban Amurka da kuma ministan harkokin wajen Jamus. Bayan mummunar gurbacewar da aka fuskanta ga yanayin dangantakun Amurka da Jamus, a yanzun al’amura sun fara komawa yadda aka saba a zamanin baya. Sassan biyu suna musayar rahotanni da bayanai tsakaninsu ba tare da wata rufa-rufa ba. Amurka ta kai ganon cewar ko da yake ita ce babbar daular da ta rage a duniya, amma fa ba zata iya warware matsalolin dake addabar duniyar ita kadai ba, kuma tilas ne ta canza salon kamun ludayinta a dangantakarta da kawayenta.

A ganawar da aka yi tsakanin P/M Palasdinawa Ahmad Qurei’i a bangare guda da shugaban kasar Jamus da kuma jami’an gwamnatin kasar a daya bangaren an mayar da hankali ne wajen sauraron halin da ake ciki a yankunan Palasdinawa dake da ikon cin gashin kansu. Sai kuma neman cikakken bayani a game da matsayin da Jamus da sauran kawayenta na nahiyar Turai suka sake jaddadawa baya-bayan nan na cewar kamata yayi shawarwarin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya su tafi kafada-da-kafada da matakan raya makomar yankin. Wadannan matakai wajibi ne su hada da kasashen Turai da Amurka da kuma kasashen Larabawa baki daya. Ana iya gabatar da shawara akan wannan manufa lokacin taron kolin shugabannin kasashen G8 da za a gudanar a Amurka a cikin watan yuni mai zuwa. Jamus kazalika tana iya ba da kyakkyawar gudummawa ko da yake ba zata iya daukar matakai na radin kanta ba, sai dai kawai ta kasance mai ba da sabon jini bisa manufa.