Ziyarar Premier Wen Jiabao na Sin a Congo | Labarai | DW | 19.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Premier Wen Jiabao na Sin a Congo

Kowane lokaci daga yanzu Premiern kasar Sin Wen Jiabao,zai isa janhuriyar democradiyyar congo,dake gabar gulf na guinea mai albarkatun man petur a yankin yammacin Afrika,inda kuma bukatun makamashi na kasar sin ke taimakawa inganta bunkasar mai.Ana saran shugaba Denis Sassou Nguesso na janhuyar Congo ne zai marabci,premier Wen,wanda ke rangadin kasashen Afrika guda 7,ziyarar data kaishi masar da Ghana ,kuma bayan congo,zai ziyarci Angola da Afrika ta kudu da Tanzania da kuma Uganda.Kasar Sin dai nada muradin mai kwarai da gasket,kasancewar ingantuwan tattalin arzikinta dake dada bunkasa na wakiltar daya daga cikin masu amfani da makamashi.Janhuriyar congo wanda ke bangaren Guinea,dake iyaka da Nigeria mai albarkatun mai a yankin,na kyautata zaton samarda ganga million 13.8 na danyan mai,a shekaran nan da muke ciki.

 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6c
 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6c