1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Paparoma a Mexico

March 24, 2012

Dubunan jama'a sun yi dafifi kan titunan Mexico domin yin lale marhabin ga Paparoma Benedikt na 16

https://p.dw.com/p/14R45
Pope Benedict (C) is welcomed by Mexican President Felipe Calderon (R) and his wife Margarita Zavala after the Pontiff arrived at the Guanajuato International Airport at the start of his trip to Mexico March 23, 2012. Pope Benedict landed in Mexico on Friday promising to send out a strong message against drug cartels in a country convulsed by a surge in gang violence over the past five years. REUTERS/Tony Gentile (MEXICO - Tags: RELIGION POLITICS) (eingest. SC)
Paparoma tare da shugaban Mexiko da mai dakinsaHoto: Reuters

Shugaban darikar Roman Katolika na duniya, ya fara rangadin kwanaki uku irinsa na farko a kasashen yankin Latine Amurika masu amfani da halshen spananci.

A Mexico dake matsayin matakin farko Paparoma ya samu gagaramin tarbe.

A kan hanyarsa ta zuwa kasar Mexico, dake matsayi ta biyu wajen yawan kiristoci mabiya darikar Roman katolila, Benedikt na 16 ya bayyana wajibcin daina safara miyagun kwayoyi, wanda kasar ta yi fice akai.

Kiddidigar ta nuna cewa, fiye da mutane dubu 50 suka rasa rayuka a shekarun baya-bayan nan, dalili da yake-yake tsakanin manyan diloli kwaya, abinda ya dushe tarmamuwar shugaba Felipe Calderon na Mexico, wanda zai fuskanci saban zaben shugaban kasa a watan Juli na wannan shekara.

Dubunan jama'a ake sa aran za su halarci sallar da Paparoma zai jagoranta gobe idan Alah ya nuna mana.

Bayan Mexiko Benedikt na 16 zai ziyaraci kasar Cuba ranar Litinin mai zuwa inda zai kara karfin gwiwar ga mahunkuntan kasar, suka kara himmantuwa wajen shimfida tafarkin demokradiya da kuma kara samun nutsuwa cikin imani.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala