1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Paparoma a Malta

April 18, 2010

Paparoma Benedikt na 16 ya jagoranci bikin addu'o'i a tsibirin Malta

https://p.dw.com/p/MzgR
Paparoma Benedikt na 16 da shugaban Malta George AbelaHoto: AP

Paparoma Benedikt na 16 ya yi kira ga al'ummar ƙasar Malta da su ƙarfafa imaninsu tare da gujewa aikata alfasha. Paparoman ya yi wannan kira ne a wani bikin addu'o'i da ya jagoranta, inda dubbanen mabiya addinin Kirista suka hallara duk da yayyafi da aka yi ta yi. Sun nuna masa goyon bayansu yayin huɗubar ta sa wadda ta zo a rana ta biyu kuma ta ƙarshe a ziyarar da ya kai wannan ƙasa wadda mai yawan mabiya ɗarikar Katholika.

"Ba dukkan abubuwan da ake gani a duniya ne suke da daraja ba. Abubuwa da dama na ƙoƙarin karkata hankulanmu daga imani da Ubangiji domin mu ƙauracewa coci kana mu bi tunaninmu kan yadda za mu tafiyar da rayuwarmu. Suna gaya mana cewa ba ma buƙatar Allah da kuma wurin ibada."

A ganawarsa da Paparoma a jiya shugaban ƙasar Malta George Abela ya ta da batun lalata da yara da wasu malaman cocin Katholika suka yi. Shugaba Abela ya yi nuni da wata shari'ar da ake wa wasu limaman majami'ar Katholika su uku, waɗanda ake zarginsu da yin lalata da yara marayu. Ya ce dole ne a yi adalci a wannan shari'a da ake yi a tsibirin na Malta.

A halin da ake ciki Paparoma ya gana da waɗanda aka ci zarafinsun a Malta kuma yayi musu alƙawarin ɗaukar matakai mafi dacewa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi