Ziyarar Obama a Ghana | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ziyarar Obama a Ghana

Ziyarar farko da shugaban Amirka Barak Obama ya kai Ghana shi ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus

default

Obama da Uwargidansa a Ghana

A wannan makon dai ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a game da nahiyar Afurka shi ne ziyarar da shugaban kasar Amurka Barak Obama ya kai kasar Ghana a ƙarshen makon da ya wuce, inda ya gabatar da jawabi ga wakilan majalisar dokokin ƙasar ya kuma ziyarci wasu wurare na tarihi. A lokacin da take gabatar da rahoto game da haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

Barack Obama in Ghana Afrika

"A cikin jawabin da ya gabatar gaban majalisar dokokin Ghana, shugaban Amurka Barak Obama ya taɓo batun da har yau nahiyar Afurka ke fama da raɗaɗinsa, sannan ya ƙara tabbatar da cewar wajibi ne su kansu ƙasashen Afurka su tashi tsaye su ɗauki ƙaddararsu a hannunsu. Kazalika shugaban yayi kakkausan suka akan matsalar cin hanci da ta zama ruwan dare a ƙasashen Afurka, wadda ya ce ita ce ainihin ummalaba'isin koma bayan da nahiyar ke fama da shi. Shugaban dai yayi wa ƙasashen Afurka alƙawarin daidaita ma'amallarsu da Amurka."

To sai dai kuma ita jaridar Der Tagesspiegel a cikin nata rahoton cewa tayi:

BdT Barack Obama in Ghana Afrika

Lale da Obama a Ghana

"Wannan alƙawari da Obama yayi, bisa ga ra'ayin manazarta, ba zai kawo wani canji na a zo a gani a game da manufofin Amurka dangane da nahiyar Afurka ba. Dalilin haka kuwa shi ne kasancewar magabacin Obama tsofon shugaban Amurka George W. Bush yana da farin jini a sassa da dama na Afurka sakamakon bunƙasa yawan kuɗaɗen taimakon raya ƙasar da yayi, musamman a matakan yaƙi da cutar Aids mai garya garkuwar jikin ɗan-Adam."

A wani kyakkyawan ci gaba da ake samu ƙasar Burundi an fara hangen samun zaman lafiya mai ɗorewa bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru da dama. Jaridar Die Tageszeitung tayi bayani akan haka tana mai cewar:

Kindersoldaten - Burundi

Ƙaramin soji a Burundi

"Bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru 16 rukuni na ƙarshe na 'yan tawayen ƙasar Burundi sun muƙa makamansu ga mahukunta. A cikin watan afrilun da ya wuce ne shi kansa madugun 'yan tawayen ya miƙa nasa makamin na Kalashinikov don zama wata kyakkyawar alama ta sanin ya kamata da sauran magoya bayansa zasu yi koyi da shi. A nata ɓangaren ƙungiyar tarayyar Turai ta taimaka aka giggina wasu ƙuyuka ashirin don tsugunar da 'yan tawayen dake dawowa gida bisa manufar tabbatar da zaman lafiyar ƙasar dake ƙuryar tsakiyar Afurka."

Bayan katsewa ta tsawon watanni shida, a wannan makon an sake komawa ga shari'ar tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor a birnin The Hague. A rahoton da ta bayar game da haka, jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

Kriegsverbrecher Charles Taylor

Tsohon shugaban Liberiya Charles Taylor

"A dai halin da ake ciki yanzu ba za a iya yin hasashen yadda zata kaya a shari'ar ba. Domin kuwa lauyan dake kare Taylor ya gabatar da sunayen mutane 249, da suka haɗa har da wasu shuagabannin Afurka da jami'an diplomasiyyar majalisar ɗinkin duniya, waɗanda ya ce yana bukatar ya saurari shaidarsu."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal