Ziyarar Mr Zoellick a Nahiyar Afrika | Siyasa | DW | 26.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Mr Zoellick a Nahiyar Afrika

ƙoƙarin Bankin Duniya na yaƙi da matsalar talauci a ƙasashen Afrika

default

Tallafin raya ƙasa ga ´yan gudun hijira a Kongo

Batun talauci da koma bayan da yawa daga cikin ƙasashen Nahiyar Afrika, abune dake ɗaya daga cikin manyan batutuwa, dake ɗaukar hankalin mahalarta taron tattalin arziƙi na Duniya, a can birnin Davos na ƙasar Siwizland.

  A yayin da ake kammala wannan taro a yau, shugaban Bankin Duniya Mr Robert Zoellick kira ya ɗaukaka ga mahalarta taron na sa kaimi, wajen ci gaba da yaƙi da matsalar nan ta Talauci da kuma Yunwa da a yanzu haka ke addabar da yawa daga cikin al´umman Duniya, musanmamma a Nahiyar Afrika. Ƙin aiwatar da wannan batu a cewar Mr Zoellick, abune da ka iya mayar da hannun agogo baya, dangane da matakan raya ƙasa da hukumomi da ƙasashe suka sako a gaba.

Rahotanni sun shaidar da cewa a mako mai zuwa ne, Mr Zoellick zai yi balaguro izuwa Afrika, don ziyarar ƙasashe huɗu da suka haɗar da Maurtaniya da Liberiya da Mozambique da kuma Habasha.

   Ziyarar ta Mr Zoellick za ta zo ne, a dai-dai lokacin da da yawa daga cikin ƙasashe a Nahiyar ta ke fuskantar matsaloli na tashin gwauron zabin harkokin makamashi, duk kuwa da cewa a shekarar data gabata, mafi akasarin ƙasashen sun samu nasarar sai-saita linzamin tattalin arziƙin ƙasashen, a hannu ɗaya kuma da biyan da yawa daga cikin bashin da Bankin Duniya ke binsu. To ko shin ta ya ya Bankin na Duniya zai fuskanci wannan ƙalubale? Mr Robert Zoellick ya yi ƙarin haske da cewar:

´´ Na farko dai akwai buƙatar ƙasashen shinfiɗa kyakkyawan mulki bisa tabarmar adalci, wanda hakan zai taimaka, wajen yaƙi da matsalar nan ta cin hanci da rashawa. Samun hakan zai assasa isar ayyukan raya ƙasa ga mabuƙata. A don haka za muyi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙasashen dake fuskantar wannan matsala don samo bakin zaren´´


  A yanzu haka dai rahotanni sun nunar da cewa ƙasar Sin na taka muhimmiyar rawa, wajen ci gaban tattalin arziƙin da dama daga cikin ƙasashen Afrika. Hakan na faruwa ne ta yadda ƙasar ke ci gaba da faɗaɗa zuba hannun jarinta ne, a kamfaninnika da masana´antu dake Nahiyar. Ko shin ya ya Bankin na Duniya ke kallon irin wannan rawa da Sin ke takawa a Afrika, a hannu ɗaya kuma da abinda hakan ka iya haifarwa a fage na tattalin arziƙin Duniya? Shugaban Bankin na Duniya, Mr Robert Zoellick ya ci gaba da cewar:


 ´´ Mr Zoellick ya ce  ƙasar Sin babu shakka na samun bunƙasar tattalin arziƙi a Duniya, dangane da yadda take zuba hannun jari da yawan gaske a Afrika, to amma hakan ka iya zama alfanu ga Nahiyar ne kawai, idan matakin ba zai janyowa ƙasashen tulin tarin bashi ba. Bankin Duniya zai ci gaba da aiki tare da ƙasar Sin, wajen cimma manufa, a fannoni na raya ƙasa da cinikayya da sauransu´´

Shekaru 60 da kafuwar Bankin na Duniya, rahotanni sun shaidar da cewa babu ko ja Bankin na taka muhimmiyar rawa, wajen ci gaban da yawa daga cikin ƙasashe na Duniya, musanmamma na Nahiyar Afrika dake ci gaba da fuskantar matsaloli na koma bayan tattalin arziƙi, sakamakon matsalolin yaƙe-yaƙe da cin hanci da rashawa da makamantansu. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito shugaban Bankin na Duniya na tabbatar da cewa matakan Bankin na yaƙi da matsalar cin hanci da rashawa ga Nahiyar Afrika na nan daram:

 ´´ Mr Zoellick ya ce matakin Bankin Duniya na ci gaba da yaƙi da matsalar talauci na nan daram. Bankin na ci da da ɗaukar sabbin matakan na yaƙi da wannan matsala, musanmanma ga ƙasashe da suka fuskanci matsaloli na rikice-rikice irinsu Liberiya da Ivory Coast da Afghanistan da makamantansu´´