Ziyarar Mr Cheny a Afghanistan ta ci karo da tashin bom | Labarai | DW | 27.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Mr Cheny a Afghanistan ta ci karo da tashin bom

Mataimakin shugaban kasar Amurka, Dick Cheney na ci gaba da ziyarar aiki a Afghanistan. A wani lokaci a nan gaba a yau, Mr Cheney zai gana da kwamdojin Amurka dake gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a kasar.

Bugu da kari ana sa ran kafin kammala ziyarar Mr Dick Cheney zai yi ganawar ido da ido da shugaba Hamid Kharzai.

Rahotanni dai daga kasar sun shaidar da tashin wani bom a kofar cibiyar dakarun sojin Amurka dake kasar.

Hakan dai ya haifar da asarar rayuka biyu da kuma jikkata wasu.

To sai dai ya zuwa yanzu tashin bom din a cewar bayanai baya wata barazana ga ziyarar da Mr Cheney yake a kasar.

A dai jiya ne Mr Cheney ya kai wata ziyarar ba zata izuwa Pakistan, a inda ya gana da Shugaba Pavez Musharraf.

A lokacin ganawar , Mr Cheney ya bukaci shugaban na Pakistan daya ci gaba da yaki da ayyukan yan ta´adda, dake ci gaba da fadada ayyukan su a iyakar kasar da Afgahanistan.