1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung a Afghanistan

Ministan ya yaba da ƙarfin hali da kuma namijin aikin da sojojin rundunar Jamus ta Bundeswehr ke yi a Afghanistan

default

Ministan tsaro Franz Josef Jung a Kundus


Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya kai wata ziyara a Afghanistan don nema ƙarin bayani dangane da halin da ake ciki a can. A ganawar da yayi da sojojin Jamus a garin Kunduz dake arewacin ƙasar ta Afghanistan, mista Jung ya yaba da aikinsu sannan ya bayyana halin da ake ciki a yankin da cewa abin damuwa ne.


A ziyarar da ya kai a sansanin dakarun Jamus a garin Kunduz ministan tsaron na Jamus Franz Josef Jung ya yaba da ƙarfin zuciyar sojojin.


Ya ce: "Haƙiƙa yanzu ana cikin wani hali na rashin sanin tabbas. Abin damuwa ne ganin yadda masu kai hare haren ƙunar baƙin wake suka ƙaru a wannan yanki. Amma ina mai godiya kuma ina alfahari da namijin aikin da sojojinmu ke yi a nan. Suna da ƙwarewar aiki sannan suna da kayan aiki. Duk da wannan hali na zullumi su na da ƙwarin guiwar gudanar da aikinsu."


Labaran da ake samu a kullum na tabbatar da irin mawuyacin halin da ake ciki musamman dangane da kaiwa sojojin na Jamus hare haren kunar baƙin wake. Alal misali a ranar Litinin wani ɗan ƙunar bakin wake ya tarwatsa kanshi a kusa da sojojin Jamus dake sintiri. To amma sojojin sun tsira. Wani soja ya yi wa ministan tsaron bayani irin zama na fargaba da suke ciki a kullum.


Ya ce: "A kullum muna samun gargaɗi dangane da yiwuwar kai mana hari muna ɗaukar waɗannan labarai da muhimmanci shi ya sa a kullum muna kansancewa cikin shirin ko-takwana."


A garin Kunduz mista Jung ya kuma gana da gwamnan lardin Injiniya Mohammed Omar da kuma shugaban ƙabilar Pashtun wanda ya a makon da ya gabata ya yi sulhu tsakanin sojojin rundunar Bundeswehr da kuma iyalan mutanen nan uku da sojojin Jamus suka kashe a ranar Alhamis da ta gabata. Wannan lamari ya auku lokacin da motarsu ta ƙi tsayawa a wani wurin binciken ababan hawa dake ƙarƙashin kulawar sojojin Afghanistan da na Jamus duk da harbin gargaɗi da aka yi. A dangane da haɗarin da ka iya rutsa da su sojojin sun buɗe wuta kan motar inda suka kashe mace guda da yara biyu. Gwamnan ya ba da tabbacin cewa ba wanda ya zargi Jamusawan da halaka mutanen da gangan. Yanzu dai za a warware wannan batu ta hanyar biyan diyya don hana ɗaukar fansa kan Jamusawan kamar yadda ministan ya ƙarfafa.


Ya ce: "Burin mu shi ne mu taimakawa mutanen don a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. Za mu yi iya ƙoƙarin mu don ƙauracewa sake aukuwar birin wannan haɗari dake rutsawa da fararen hula."


Ko da yake Jamus na ƙoƙrtawa wajen horas da jami´an tsaron yankin, amma har yanzu da sauran jan aiki a gaba.