Ziyarar Ministan tsaron Jamus a yankin Asia | Labarai | DW | 19.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Ministan tsaron Jamus a yankin Asia

Ministan harkokin tsaro na tarayyar jamus Franz Josef Jung yana birnin Tokyo,fadar gwamnatin kasar japan domin ganawa da takwaransa Fumio Kyuma.Ana kyautata zaton cewa Mr Jung zaiyi amfani da damar wannan tattaunawa nasu, wajen bukatar jaddada dangantakar dake tsakanin Jamus da Japan musamman adangane da kasar Afganistan.Japan dai na zama kasa ta biyu da ministan tsaron na jamus ya sa kafa,acigaba da rangadin aikin daykeyi a yankin Asia,ziyarar da zata kaishi zuwa koriya ta Arewa.A jiya a birnin Beijing din kasar Sin,Mr Jung ya cimma yarjejeya da magabatan kasar,adangane da daukan tsauraran matakai kan batutuwa da suka shafi tsaro.