Ziyarar Ministan tsaron Jamus a Afrika
September 25, 2006Talla
Ministan tsaro na nan Jamus Franz Joseph Jung na cigaba da ziyarar kwanaki uku a ƙasashen Afrika, inda zai ziyarci sojojin Jamus a nahiyar. Ministan zai kai ziyara Djibouti da Gabon da kuma jamhuriyar dimokraɗiyar Congo. Joseph Jung ya fara yada zango a Djibouti inda sojojin Jamus kimanin 350 ke taimakawa ƙasar wajen tsaron kan iyakokin ruwa a matakan yaƙi da yan tarzoma. Zai kuma gana da shugaban ƙasar Congo Joseph Kabila da kuma madugun adawa Jean Pierre Bemba.