Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus Joschka Fischer Ga Kasar Sudan | Siyasa | DW | 12.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus Joschka Fischer Ga Kasar Sudan

A yammacin jiya lahadi ne ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya sauka birnin Khartoum domin tattaunawa da jami'an gwamnatin kasar Sudan akan mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur, wanda rikicinsa ya ki ci ya ki cinyewa

Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer a Sudan

Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer a Sudan

Tun da farkon fari ministan harkokin wajen na Jamus Joschka Fischer ya fito fili ya bayyana kaunar ganin cewar gwamnagtin Sudan ta dauki nagartattun matakai na shawo kan rikicin lardin Darfur a siyasance, inda ya yi bayanin cewar:

Wannan maganar ta shafi kwance damarar dakarun sa kai da kuma gurfanar da masu miyagun laifuka na ta’asar rikicin gaban kotu ba da wata-wata ba. A baya ga haka wajibi ne a ba wa kungiyoyin taimakon jinkai cikakkiyar dama domin kai gudummawa ga mutanen dake fuskantar barazana game da makomar rayuwarsu.

A ganawarsu ta yau litinin Fischer ya gabatarwa da shugaba E-Bashir da ministan harkokin waje Isma’il da kuma mataimakin shugaban kasar Sudan Taha, wannan matsalar dake ci masa tuwo a kwarya. Bisa ga ra’ayin ministan harkokin wajen na Jamus, gwamnatin Sudan ce kawai ke da ikon magance wannan rikici ta hanyar sake maido da doka da oda a wannan yanki. Lokaci dai sai dada kurewa yake yi ganin yadda damina ke karatowa kuma dubban daruruwan mutane na fama da yunwa. Akwai bukatar daukar nagartattun matakai domin hana wanzuwar wani mummunan bala’i in ji Kerstin Müller, karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, wacce ke wa Fischer rakiya. Ta ce tana so ta gane wa idanuwanta abin dake faruwa a Darfur, inda dubban daruruwan mutane suka tagayyara a cikin hali na rashin sanin tabbas game da makomarsu sakamakon bannatar da kauyukansu da dakarun Janjaweed suka yi. Wadannan dakarun Larabawa jajayen fatu suna samun goyan baya daga gwamnatin tsakiya a fadar mulki ta Khartoum. Manufarsu ita ce su karya alkadarin bakar fata dake neman karin ikon cin gashin kansu a lardin Darfur. A baya ga haka akwai gwagwarmayar dora hannu akan filayen noma da albarkar ruwa. An dai saurara daga bakin ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yana mai nuna cewar abin da gwamnati a nan Jamus ke ba wa fifiko shi ne matakai na diplomasiyya duk da cewar har yau gwamnatin Sudan na ci gaba da yin kunnen-uwar shegu da matsin lambar da take fuskanta daga ketare. Kuma ko da yake a halin yanzu haka kwamitin sulhu na MDD na shawartawa a game da wani kudurin da za a zartas akan kasar Sudan, amma akwai kasashe da dama dake adawa da kakaba wa fadar mulki ta Khartoum matakai na takunkumi. Ko shakka babu sakamakon shawarwarin da Fischer zai gudanar a Khartoum zai yi tasiri akan kudurin na kwamitin sulhu. Kazalika a ziyarar da aka shirya zai ci gaba da kaiwa ga kasashen Asiya, ministan harkokin wajen na Jamus zai tattauna wannan batu da wakilan gwamnatocin kasashen China da Pakistan wadanda kawo yanzu suke dari-dari da shawarar takunkumin akan kasar Sudan. Ita kanta ziyararsa ga Sudan tana da nufin ci gaba da matsin kaimi akan fadar mulki ta Khartoum, bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell da sakatare-janar na MDD Kofi Annan suka kai kasar ta Sudan makon da ya gabata.