Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus a Afghanistan | Siyasa | DW | 21.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus a Afghanistan

A ziyararsa ga kasar Afghanistan ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi wa shugabannin kasar alkawarin ci gaba da samun taimako daga Jamus a fafutukar sake gina kasar da ya ki yayi kaca-kaca da ita

Joschka Fischer lokacin da yake rangadin sojan Jamus a Kunduz a arewacin Afghanistan

Joschka Fischer lokacin da yake rangadin sojan Jamus a Kunduz a arewacin Afghanistan

A cikin jawabin da ya gabatar a birnin Kabul ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi kira ga sauran kasashe da su ba da tasu gudummawar iya gwargwado a matakan sake gina kasar Afghanistan. Ya ce wannan mataki yana da muhimmanci matuka ainun domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma zaben kasar da aka shirya gudanarwa nan da karshen wannan shekara. A nasu bangaren wakilan kasar Afghanistan sun yaba da irin rawar da tawagar taimakon sake gina kasar Afghanistan ta Jamus ke takawa a Kunduz. Gwamnan lardin Muhammed Omar ya mika cikakkiyar godiya game da taimakon da Jamus ke bayarwa. A mayar da martani Fischer ya ce taimakon da kasar ke bayarwa na dogon lokaci ne. Shi kansa Fischer sai da ya bayyana gamsuwarsa da kakkarfan hadin kan dake akwai tsakanin sojojin Jamus da jami’an diplomasiyya da kuma jami’anta na taimakon raya kasa a lardin Kunduz, bayan balaguron yankin da yayi har tsawon sa’o’i uku. A halin yanzu haka tawagar taimakon sake ginawar ta Jamus ta fara shawarar fadada ayyukanta domin su hada da wasu yankuna dake wajen Kunduz. A lokacin ganawarsa da Hamid Karzai a Kabul kuwa, shugaban na kasar Afghanistan ya sake nanata godiyarsa ne ga Fischer dangane da irin rawar da Jamus ta taka wajen shirya taron Afghanistan, wanda aka gudanar karo na uku a harabar Jamus, misalin makonni uku da suka wuce. Shugaban ya ce ana ci gaba da rajistar masu zabe, musamman mata, ba tare da wata tangarda ba. Mutane kimanin miliyan daya da dubu dari takwas ne suka yi rajista kawo yanzu kuma ana fata adadin zai kai mutum miliyan tara kafin wa’adin rajistar ya cika. A lokacin ziyarar tasa ga Afghanistan Joschka Fischer, wanda tuni ya zarce zuwa kasar Azerbaijan, yayi nuni da muhimmancin zaben da aka shirya gudanarwa watan satumba mai zuwa. A yayinda aka fuskance shi da tambaya lokacin wani taron manema labarai a birnin Kabul a game da ko shin an makara wajen koyan darasi daga Afghanistan dangane da makomar kasar Iraki, ministan harkokin wajen na Jamus nuni yayi da cewar ga alamu al’amuran Iraki na da sarkakiyar gaske fiye da na kasar Afghanistan. To sai dai kuma ko da yake an bata lokaci da yawa, amma ana iya koyan darasi a koda-yaushe. Muhimmin abin dake akwai yanzun shi ne ba da cikakken goyan baya ga wakilin MDD akan al’amuran Iraki Lakhdar Brahimi. Da farko dai Brahimi, shi ne mai kula da al’amuran Afghanistan da sunan MDD kafin majalisar ta dora masa alhakin wakiltarta akan al’amuran kasar Iraki.