1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR MINISTAN HARKOKIN WAJEN IRAN, KAMAL CHARRASI, A JAMUS DA KASASHEN TURAI.

YAHAYA AHMEDMay 6, 2004

A cikin wannan makon ne, ministan harkokin wajen Iran, Kamal Charrasi, ya fara kai ziyara a wasu kasashen Turai. Ya dai fara ya da zango ne a birnin Brussels, na kasar Belgium, inda kuma nan ne kungiyar Hadin Kan Turai ke da cibiyarta, kafin ya iso a birnin Berlin jiya, inda ya gana da takwarar aikinsa na Jamus, Joschka Fischer da shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder. Iran din dai na kokarin inganta huldodinta da kasashen Turai. Amma har ila yau abin da ke hana mata ruwa gudu a wannan yunkurin, shi ne batun nan na makamashin nukiliyan da take mallaka.

https://p.dw.com/p/Bvjq
Ministan harkokin wajen Iran, Kamal Charrasi da takwarar aikinsa na Jamus, Joschka Fischer, yayin ganawarsu (ran 5 ga watan Mayu) a birnin Berlin.
Ministan harkokin wajen Iran, Kamal Charrasi da takwarar aikinsa na Jamus, Joschka Fischer, yayin ganawarsu (ran 5 ga watan Mayu) a birnin Berlin.Hoto: AP

A halin yanzu dai, da wuya a kwatanta yadda dangantaka tsakanin Jamus da Iran take. An dai sami hauhawar tsamari a cikin kwanakin bayan nan, ba ma da Jamus din kadai ba, har da kuma Kungiyar Hadin Kan Turai. Sau da yawa dai, bangarorin biyu, wato Iran da nahiyar Turai, sun sha watsad da matsloli da dama da suka kunno kai a huldodin dangantakar da ke tsakaninsu, ba tare da warware su ba. Sai daga baya ne kuma, idan wani rikicin ya taso, sai matsalolin su kara habaka.

Jigogin da Iran din da kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai ke samun bambance-bambancen ra’ayoyi a kansu, sun hada ne da batun nan na makamashin nukilyan da Iran ke mallaka, da halin da ake ciki yanzu a Gabas Ta Tsakiya. Sai kuma irin wainar da ake toyawa yanzu a kasar Iraqi, da kuma batun kare hakkin dan Adam da bin tafarkin dimukradiyya a Iran.

Duk wadannan batutuwan kuwa na da jibinta da juna. Kasashen Turai dai, sun nuna rashin gamsuwarsu ga yadda aka gudanad da zaben Majalisar dokoki a kasar Iran a cikin watan Fabrairun da ya gabata, saboda a nasu ganin, a lokacin kada kuri’ar, an take ka’idojin dimukradiyya da `yancin da kowa ke da shi na zaban wanda ya ga dama.

Har ila yau dai, sabuwar Majalisar ta Iran ba ta fara zama ba tukuna. Kuma, ba za a iya ganin sake alkibla a kasar ba, sai bayan zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar badi. Amma tun yanzu ma, wasu masu sukar lamiri na kasashen Yamma, na bayyana ra’ayin cewa, `yan ra’ayin mazan jiya a Majalisar ne, za su yi wa harkokin tafiyad da mulki a kasar babakere. Sun dai yi matashiya ne da sabunta hukuncin kisan da aka yanke wa shahin malamin jami’an nan Farfesa Aghajari. An dai zarge shi ne da cin amanar kasa, bayan ya yi kira ga yi wa tsarin zaman jama’a a Iran din garambawul. Amma saboda zanga-zangar nuna adawa ga wannan hukuncin da daliban kasar suka dinga yi, da kuma angaza wa mahunkuntan kasar da bangarorin neman sauyi na cikin gida da na ketare suka yi ne, aka yi masa afuwa. Amma sai ga shi kuma yanzu, bayan zaben Majalisar, inda `yan mazan jiyan suka sami rinjayi, an sake maido da hukuncin kisan kan shaihin malamin. kasashen Yamman dai na ganin cewa, wannan hukuncin na daya daga cikin ababan da ke hana ruwa gudu a huldodinsu da Iran.

Game da batun halin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya ma, akwai gagarumin gibi, tsakanin bangarorin biyu. Mahukuntan Teheran dai ba sa ga maciji ma da Isra’ila. Kuma suna adawa ga duk wani yunkurin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kasar ta Yahudu. Batun da bangarorin biyu za su iya cim ma daidaito a kansa ne, rikicin Iraqi. A nan Jamus dai, mahunkuntan birnin Berlin na sane da cewa, Iran za ta iya taka muhimmiyar rawar gani wajen shawo kan tashe-tashen hankulla a Iraqin, kamar dai yadda ta nuna game da Afghanistan.

Daya batun da ake ta korafi a kansa kuma, shi ne na shirin mallakar makamashin nukiliyan da Iran ta sanya a gaba. A goshin karshen shekarar bara dai, ministocin harkokin wajen Jamus, da Faransa da Birtaniya, sun cim ma nasarar shawo kan Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar hana yada makamashin nukiliya da Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya Ta kasa da kasa ta gabatar mata. Sai dai daga baya, kasashen Turan, sun zarge ta da boye musu wasau daga cikin shirye-shiryenta. Dalilin haika ne kuwa, suka sanya mata takunkumi na kin ba ta ta fasahar inganta kafofin nukiliyanta don samad da makamashi. A can Teheran kuma, mahukuntan Iran din na zarrgin Turawan ne da yaudara.

Duk da hakan dai, kasashen Turan na dari-dari da zargin da Amirka ke yi wa Iran na cewar tana yunkuri ne na mallakar makaman nukiliya. A nasu ganin, nanata irin wannan zargin da Amirkan ta yi game da Iraqi, ya kasance babu gaskiya a cikinsa.

Amma a bangare daya kuma, suna taka tsantsan wajen sakewa su bai wa Iran din fasahar da take bukata don inganta kafofinta na makamshin nukilyan.