Ziyarar Ministan Cikin Gida Na Jamus A Washington | Siyasa | DW | 11.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Ministan Cikin Gida Na Jamus A Washington

Bisa ga ra'ayin ministan cikin gida na Jamus Otto Schily tabargazar azabtar da fursinonin Iraki da aka fallasa baya-bayan nan abu ne da ya mayar da hannun agogo baya a fafutukar murkushe ta'addanci a duniya kuma abin kunya ne ga sojan taron dangi a Iraki

Ministan cikin gidan Jamus Otto Schily

Ministan cikin gidan Jamus Otto Schily

A ziyararsa ga birnin Washington, ministan cikin gida na Jamus Otto Schily bai yi wata rufa-rufa ba wajen yin tofin Allah tsine akan matakin azabtar da fursinonin yaki da sojan Amurka suka dauka a kasar Iraki, wanda ya ce wannan wani mummunan tabo ne da da kyar ne za a iya warkar da shi, saboda babu wani dalili na yin hakan. Kazalika Otto Schily yayi kakkausan suka a game da halin da fursinoni ke ciki a sansanin gwale-gwalen kasar Amurka dake tsuburin Guantanamo, inda ya ci gaba da cewar:

Wannan abin kunyar da aka fallasa baya-bayan nan a Abu Ghoraib ya kada zukatan jama’a matuka da aniya, kuma babban koma baya ne ga sojan taron dangi a kasar Iraki. Kazalika a daya bangaren, wani kalubale ne ga fafutukar murkushe ta’addanci a duniya, saboda wannan fafutukar ba zata cimma nasara ba sai ta hanyar shawarwari a siyasance. Bugu da kari kuma wannan tabargazar ta saba da dukkan manufofin da Amurka ke tinkafo dasu.

Schily, wanda ya zarce zuwa Washington domin halartar taron share fage ga taron kolin kasashen G8 da za a gudanar a Washington watan yuni mai zuwa, ya ce zai tabo wannan maganar lokacin ganawarsu a wannan taro da ya hada da ministocin cikin gida da na shari’a na kasashen da suka fi ci gaban masana’antu a duniya, a can Savanah ta Georgiya a wannan mako. Bisa ga ra’ayin ministan na cikin gidan Jamus abu mafi alheri shi ne kasar Amurka ta sake bitar shawararta a game da bijire wa yarjejeniyar nan ta kotun kasa da kasa akan miyagun laifuka na yaki a The Hague da tayi. Schily ya kara da cewar:

Abu mafi alheri ga Amurka, ta la’akari da wannan abin kunya, shi ne ta sake gabatar da tayi shiga shawarwari a game da sharuddanta na shigowa inuwar kotun ta kasa da kasa.

A lokacin taronsu na share fage ministocin harkokin cikin gidan na kasashen G8 na fatan tattaunawa a game da hanyoyin da za a bi a kyautata al’amuran tsaro a harkar sufuri tsakanin kasa da kasa. Bisa ga ra’ayin Schily matakin Amurka na daukar hoton yatsun matafiya ba zai tsinana kome ba saboda mahukuntan Amurkan ne kadai zasu tara bayanan da suka samu daga matafiyan.

Shi ma ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer, a yau talata ne ake sauraron saukarsa a birnin Washington, kuma ba shakka zai tabo maganar ci gaban da ake samu a kasar Iraki baya-bayan nan a shawarwarin da zai gudanar tare da jami’an gwamnatin shugaba Bush.