1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a Saudiya.

May 26, 2010

A yau ne shugabar gwamnatin Jamus ke ganawa da shugabannin Saudiya.

https://p.dw.com/p/NXBm
Angela Merkel, yayin ziyara a Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa karfin ta zarce zuwa Saudiya.Hoto: AP

A yau, shugbar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ke ganawa da shugabannin kamfanonnin a ƙasar Saudi Arabiya a matsayin yanki na rangadin da ta ke ci gaba da yi a yankin Gulf. Sarki Abdullah ne ya tarbe ta yayin saukarta a birnin Jidda bayan ziyarar da ta kai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. A baya ga buƙatar ƙarfafa hulɗar kasuwanci, Merkel ta yi kira ga ƙasashen wannan yanki da su taka rawar gani a ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, da kuma tattaunawar da ake yi da gwamnatin Iran. A nasa ɓangaren, Sarki Abdullah kira yayi ga Jamus da Ƙungiyar Tarayyar Turai da su shiga tattaunwa mai zurfi tare da Amirka akan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya. Sarkin ya kuma nuna goyon bayansa ga matakin ƙaƙaba ƙarin takunkumin akan Iran domin ta bayyana haƙiƙanin manufar shirinta na nukiliya.

Mawallafiya:Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu