Ziyarar Merkel a nahiyar Afirka | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Merkel a nahiyar Afirka

A yau SGJ Angela Merkel ta ke fara rangadin wasu kasashen Afirka kudu da Sahara inda za´a mayar da hankali akan ´yancin bil Adama cutar AIDS ko SIDA, hadin kan tattalin arziki da rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar Zimbabwe. Merkel zata fara yada zango ne a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia wato Habasha. Zata gabatar da jawabi a zauren KTA sannan ta tattauna da shugaban hukumar tarayyar Afirka Alpha Oumar Konare. Taron na matsayin share fage na wani taron koli tsakanin tarayyar Turai da tarayyar Afirka wanda za´a gudana a birnin Lisbon na kasar Portugal a cikin watan desamba. SG ta Jamus zata kuma ziyarci kasashen ATK da Liberia.