Ziyarar Merkel a China | Siyasa | DW | 23.10.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Merkel a China

Ingantuwar Dangantaka tsakanin Jamus da China

default

Shugabar gwamnatin Jamus Angel a Merkel a Peking.

Duk da ƙokarin da zata yi na kaucewa duk wasu al'amura da zasu tayarda saɓanin siyasa, amma a lokacin ziyarar ta ta uku da zata kai Peking ba zata kaucewa taɓo batun kare hakkin 'yan Adam a China ba. Zata sami damar hakan lokacin tattaunawa da shugaban ƙasa, Hu Jin-tao da Pirayim minista Wen Jiabao da kuma ganawar da zata yi da ƙungiyoyin kare hakkin 'Yan Adam. Ziyarar ta China kuma tazo ne sakamakon gyaruwar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, bayan da Merkel ta karɓi shugaban al'ummar Tibet, Dalai Lama a fadar ta, abin da ya kawo kace-nace a dangantakar tasu. Ranar Jumma'a shugaban gwamnatin ta Jamus zata halarci taron kolin ƙasashen Asiya da Turai a Peking, inda shugabannin ƙasashe fiye da arba'in na ƙungiyar haɗin kan Turai da Asiya zasu tattauna kan al'amuran da suka shafi dangantakar su. Babban abin da za'a maida hankali a kai dai shine rikicin kasuwnnin kuɗi da kuma ƙokarin kawo ƙarshen canjin yanayin sararin samaniya.

Lokacin ziyarar ta ta ƙarshe a Peking, Pirayim ministan China, We Jiabao ya yabi shugaban gwmanatin ta Jamus da cewa:

Kai tsaye takan fito fili tayi magana kan al'amura ba tareda rufa-rufa ba. Wannan kuwa abu ne da nake son hakan.

Angela Merkel dai tana farin cikin wannan ziyara wadda ita ce ta ukku, duk da ganin cewar an daɗe ana fama da tsamin dangantaka tsakanin China da Jamus, bayan da shugaban gwamnatin ta gana da Dalai Lama a fadar ta a watan Satumba na shekarata 2007. Dangantakar bata daidaita ba, sai da ministan harkokin waje, Frank Walter Steinmeier a farkon wannan shekara ya fito fili ya baiyana goyon bayan sa ga manufofin ƙasar China kan Tibet, ya kuma baiyana kyamar Jamus ga duk wani kokari da Tibet da Taiwan suke yi na samarwa kansu mulkin kai.

A wannan karo ana sa ran Angela Merkel zata sami marhabin sha tara ta arziki. Jakadan China a Berlin Ma Canrong yake cewa:

Gaba dai akan ce tafiu baya yawa. Har ma a wnanan karo, shgaban gwmanati zata sami karba sha tara ta arziki.

Lokacin taron kolin na kasashen Turai da Asiya a Peking, shugaban gwmanati Angela Merkel zata yi kokarin jan hankalin takwarorin ta na Asiya game da buƙatar haɗin kai domin shawo kan rikicin kasuwannin kuɗi a duniya, wanda tace hakan ba zai yiwu ba sai tare da haɗin kan ƙasashe dake kan hanyar samun ci gaban masana'antun su.

Ko da shike China bata jin raɗaɗin rikicin na harkokin kuɗi kai tsaye a jikin ta, amma ƙasar tana tsoron koma bayan tattalin arzikin ta a cikin gida. Hakan yana iya zama barazana ga kamfanoni da masana'antun Jamus dake sayar da kayaiyakin su a China. Cikin masu rakiyar Merkel a wannan ziyara har da manyan manajoji na kamfanonin Tyssen da Daimler da Siemens. Merkel tace:

Muna sane da cewar muma kanmu muna da sha'awar ganin kasar ta China ta ci gaba da bunkasa. Saboda idan tana bunkasa muna da damar kara yawan kayaiyakin da muke sayarwa a can.

Jakadan China a Berlin, Ma Canrong yace ƙasar sa tana sane da cewar Jamus ko China, cikin su babu wanda zai iya yin gaban kansa a game da harkokin ƙudi ko na tattalin arziki. Rashin fahimta kuwa ba zai kai ƙasashen ko ina ba.

Sauti da bidiyo akan labarin