1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Merkel a China

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shiga kwana na biyu na ziyararta a Beijing inda ta gana da wasu manema labarai hudu masu sukar gwamnatin kasar ta Sin.Tattaunawar Merkel da wadannan yan jarida da aka san su da fadin albarkacin bakinsu kann batutuwa da suka shafi sauye sauye na siyasa da wasu tsauraran dokokin kasar,yana wani bangare ne na wani shiri da aka bullo da shi da nufin yayata muhimmancin yancin aikin jarida.Wannan ganawa dai tazo ne kwana guda bayan Angela Merkel ta fadawa shugaban kasar China Hu Jintao cewa duniya baki daya zata sa ido kan batun kare hakkin bil adama a kasarsa a lokacin wasannin Olympics na shekara mai zuwa.