Ziyarar Merkel a Amirka | Labarai | DW | 05.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Merkel a Amirka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da shugaba George W Bush na Amurka sun nanata kudirin su cewa Amurka da Jamus ba za su yi wata hulɗa da gwamnatin Hamas ba matukar ta ki yin watsi da akidar tarzoma da kuma amincewa da ƙasar Israila. Shugaban Amurka George W Bush yace ba za su yarda da matakin raba kafa ba, a bari guda Hamas na ikrarin bin tafarkin dimokraɗiya, a daya ɓangaren kuma tana aiwatar da ayyuka na tarzoma. Da take maida jawabi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta goyi bayan adawar Bush da gwamnatocin Hamas da kuma Iran, tana mai cewa ko ƙaɗan ba zaá kyale Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. Angela Merkel tace akwai buƙatar haɗa hannu wuri guda a ƙoƙarin da ake na samar da ƙasar Palasɗinawa domin samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma gana da shugabannin yan kasuwa a birnin New York a yayin ziyarar da ta a kasar Amurka. Merkel tace Jamus ta buɗe kofofin ta na kasuwanci ga yan kasuwar Amurka domin zuba jari.