Ziyarar mataimakin shugaban Amurka a Pakistan | Labarai | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar mataimakin shugaban Amurka a Pakistan

Mataimakin shugaban kasar Amurka, wato Dick Cheney ya kai wata ziyarar gani da ido ga guraren da balain girgizar kasa ya rutsa dasu a kasar Pakistan.

Dick Cheney, wanda ya ganewa idon sa irin barnar data faru a wadan nan yankuna, ya kara mika sakon ta´aziyyar Amurka ga shugaba Pervez Musharraf game da asarar rayukan da akayi sama da dubu 73.

Bugu da kari, Cheney ya kuma yabawa sojojin Amurka dake bayar da agajin gaggawa ga wadanda wannan balai ya rutsa dasu.

Wadan nan sojoji dai sun kasance masu jigilar mutane a abinci a kana nan jirage daga guri izuwa guri a kasar ta Pakistan a tumn lokacin da wannan abu ya faru kawo yanzu.

Bayanai dai sun nunar da cewa kasar ta Amurka ta kasance kasa data kasan ce a mataki na farko a yawan tallafi na masu gidan rana da aka bawa Kasar ta Pakistan don gudanar da aiyukan takllafi ga mutanen da wannan balai ya rutsa dasu.