1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Majalisar Dinkin Duniya a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2017

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fara wata ziyarar aiki a yankunan da ke tsananin bukatar taimako sakamakon rikicin Boko Haram a kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2YbMs
Daruruwan yara na fuskantar barazanar yunwa a kasashen Afirka da ke fama da rikici.
Daruruwan yara na fuskantar barazanar yunwa a kasashen Afirka da ke fama da rikici.Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Harnik

Rahotanni sun nunar da cewa miliyoyin mutane ne ke fuskantar tsananin barazanar yunwa sakamakon wannan rikici da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma tare da tilasta wasu masu tarin yawa zuwa gudun hijira, a wasu kasashe da ke yankin Tafkin Chadi. Da yake jawabi ga manema labarai jakadan Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniyar, Matthew Rycroft ya nunar da cewa sun fara ziyarar ne domin nuna wa al'ummar da ke cikin halin tasku cewa ba a manta da su ba. Majalisar Dinkin Duniya dai ta kaddamar da asusun tallafi na dalar Amirka biliyan hudu ga yankunan da rikicin ya shafa a Najeriya, kana ta kaddamar da makamancin wannan tallafi ga Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Yemen da suma ke fama da yakin wanda ya haddasa tsananin barazana ta yunwa a cikinsu.