Ziyarar Mahamud Ahmadinedjad a Lebanan
October 13, 2010Sugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinejad ya gabatar da zazzafan jawabi a ziyara aikin da ya kai ƙasar Lebanon,inda ya bayyana cikkaken goyan bayan ga yaƙar Israel wadda ya ce ta mamaye Lebanon da Syria.Shugaban ya yi kira ga al´umar Lebanan ta tashi tsaye tsayin daka domin korar a ta bakinsa, haramtaciyar ƙasar Israela daga yankunan da ta mamaye.
A jiya ya gana da takwaransa Michel Suleiman, inda su yi masanyar ra´ayoi game da halin da ake ciki a rikicin Gabas ta Tsakiya, da kuma sauran batutuwa da su ka shafi ma´amila tsakanin ƙasashensu biyu.
Wannan itace ziyara farko da shugaban Iran ya kai Lebanon tun hawansa karagar mulki a sherkara 2005.
Sakatariyar harakokin wajen Amurika Hillary Clinton ta yi Allah wadai da wannan ziyara wadda ta ke wa kallon wata hanya ta maida hannun agogo baya a yunƙurin samar da zaman lafiya a ƙasar Lebanon.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita :Ahmad Tijani Lawal