Ziyarar Músaveni a Jamus
June 16, 2007Talla
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel tace kasar Jamus tana bukatar kara karfafa hadin kai a fannin tattalin arziki tsakaninta da kasar Uganda.
Merkel ta fadi haka ne a lokacinda shugaban kasar Ugandan Yoweri Musaveni ya kawo ziyara nan Jamus.
Shugabar ta Jamus tace ta hango albarkatu a fannonin makamashi da ilmi.
A nashi bangare shugaba Musaveni yace kasar Uganda tana neman hanyoyin tallata nata albarkatu a kasashen ketare.