ZIYARAR KUNGIYAR MANEMAN LABARAN KUDANCIN AFIRKA A KASAR ZIMBABWE. | Siyasa | DW | 05.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR KUNGIYAR MANEMAN LABARAN KUDANCIN AFIRKA A KASAR ZIMBABWE.

Kafofin yada labarai na cikin bangarorin da sabbin dokokin da gwamnatin Zimbabwe ta zartar, suka fi shafa. A kawanakin bayan nan ne wata tawagar kungiyar maneman labarai na kudancin Afirka, wato MISA a takaice, ta kai ziyara a kasar, don gano wa idanunta irin matsalolin da kafofin yada labaran ke huskanta.

Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe.

Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe.

Wata tawagar kungiyar maneman labarai na kudancin Afirka, wato MISA, ta kai wata ziyarar fadakad da kai a birnin Harare na kasar Zimbabwe a kwanakin bayan nan, don gano wa idanunta, yaddda harkokin yada labarai a kasar ke gudana, sakamakon tsauraran matakan da gwamnatin shugaba Mugabe ta dauka na kayyade `yancin maneman labarai a kasar. Gidauniyar Friedrich-Ebert-Stiftung ta nan Jamus, wadda ke goyon bayan manufar tabbatar wa maneman labarai `yancin fadar albarkacin bakinsu a kudancin Afirkan ce, ta dauki nauyi wannan ziyarar da tawagar ta kungiyar MISA ta kai a Zimbabwen.

Fernando Goncalves, cif-edita na jaridar nan Savana ta kasar Mozambique, wanda ke cikin tawagar, ya bayyana ra’ayinsa game da halin da ke ciki a Zimbabwen ne kamar haka:-

"Ita dai kasar Zimbabwe na cikin kungiyarmu ta wannan yankin. Kuma da akwai wata huldar zumunci tsakaninmu a nan kudancin Afirka. Amma a kshin gaskiya dai, takwarornimu na huskantar matsaloli da dama a Zimbabwen. Mu kuma, a matsayinmu na kungiyar wannan yankin, ba za mu iya zaman oho ba ruwanmu ba, musamman ma dai idan takwarorinmu da ke can suka nemi taimako daga gunmu. Kamata ya yi, mu dau waszu matakai, idan muka ga yadda ake addabar da jama’a."

A cikin rahoton da tawagar ta buga dai, ta ce ba ta sami hadin gwiwar kafofin yada labarai na hukumar kasar ba, a lokacin ziyararta. Sabili da haka, `yan tawagar ba su iya sun tabbatar ko kuma karyata duk zargin da ake yi wa gwamnatin kasar na take hakkin `yan jaridu ba. Sai dai sun gano cewa, `yan adawa na huskantar matukar matsin lamba. Ba sa iya bayyana ra’ayoyinsu a kafofin yada labaran hukuma. A gidajen redioy da na talabijin din kasar, ba a samun damar bayyana ra’ayoyi daban-daban. Sauran kamfanonin jaridu masu zaman kansu da ba a haramta musu buga jaridunsu ba tukuna, ba su da karfin yada angizonsu a duk fadin kasar. A halin yanzu ma dai rahoton ya ce, kamfanonin jaridu masu zaman kansu 3 kawai ne ke aiki a kasar. Dokar ta baci da aka kafa a kasar ta sa jama’a duk sun tsorata, wajen fadar albarkacin bakinsu. Pamela Dube, cif editar wata mujallar Mokgosi ta kasar Botswana, wadda kuma ke cikin tawagar, ta bayyana cewa:-

"Wadannan dokokin dai na sa mu tuna da lokacin mulkin wariya ne a Afirka Ta Kudu. An haramta wa ko mutane 4 ma su taru wuri daya, ba da izinin `yan sanda ba. To ai wannan kuwa, kamar lokacin mulkin Apartheid ke nan. A nan kuwa, kamata ya yi mu dau matakai na ganin cewa, kafofin yada labaran kasa, suna da cikakken `yancinsu, ba su zamo mallakar wata gwamnati ba. Da can dai, kafofin yada labarai a Zimbabwe sun taka muhimmiyar rawar gani. Amma a yanzu, sai koma baya kawai suke huskanta, kuma ga shi sai kara muzguna musu ake ta yi."

Ita dai Pamela Dube ta bayyana fargabarta game da anngizon da wannan halin a Zimbabwe zai samu a kann duk yanki na kudancin Afirka. Tawagar dai ta buga cikakken rahoto ne mai shafi 22 kan danniya da barazanar da ake yi wa maneman labarai a kasar ta Zimbabwe. A ganinta kuma, da wuya a ce za a iya shirya zabe cikin kwanciyar hankali da kuma adalci a Zimbabwen, idan aka yi la’akari da yadda ababa ke wakana a kasar a halin yanzu. Amma duk da hakan, ta kyautata zaton cewa, kurar rikicin kasar za ta lafa nan ba da dadewa ba. Idan ko hakan ya samu, to babu shakka, zabe a kasar zai iya gudana cikin adalci, ba tare da an tabka magudi ba.

Ba dai duk maneman labaran kasar Zimbabwen ne suka amince da wannan ra’ayin ba. Basildon Beta, wwani dan jarridar kasar ne da yake zaman guduun hijira a Afirka Ta Kudu. Ya bayyana cewa:-

"Ba zan iya amincewa da wannan ra’ayin ba. Ko da ma shugaba Mugabe ya aiwatad da duk canje-canjen da ya gabatar, hakan ba zai haifad da wani sakamako ba. Ba mu da wata muhimmiyar kafar yada labarrai kuma. kungiyoyin adawa, ba su da damar yin amfani da hanyoyin sadaswa na zamani. Bugu da kari kuma, sabbin dokokin da aka zartar sun kara matsa wa kugiyoyin adawar lamba, ta yadda ba za su iya gudanad da yakin neman zabe ba. A cikin wannan hali, ban ga yadda za a iya cewa, za a gudanad da zabe da nuna adalci ba."

 • Kwanan wata 05.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhW
 • Kwanan wata 05.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhW