1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Kofi Annan a Nijer

August 24, 2005

Bayan saukarsa a kasar Nijer sakatare-janar na MDD Kofi Annan bai yi wata-wata ba wajen kai ziyara ga yanukunan kasar dake fama da yunwa

https://p.dw.com/p/BvaH
Annan ya kai ziyara asibitin yara a Nijer
Annan ya kai ziyara asibitin yara a NijerHoto: AP

Ziyarar ta sakatare-janar Kofi Annan ga kasar Nijer tana da nufin karya alkadarin masu sukan lamirin MDD ne a game da rashin tabuka kome wajen taimaka wa yankunan da bala’i daga Indallahi kann rutsa dasu. Kungiyar likitoci ta kasa da kasa tana zargin cewar kayan taimakon da ake gabatarwa basa isa ga mabukata, kuma MDD tayi sako-sako wajen mayar da martani akan bala’in yunwar a kasar Nijer. To sai dai kuma ba za a iya dora wa majalisar laifin wannan sako-sako da tayi da lamarin ba saboda ita kanta gwamnatin Nijer da farkon fari ta yi wa matsalar rikon sakainar kashi inda ta rika karyata rahotannin cewar kasar na fuskantar yunwa. Hatta a wannan halin da muke ciki yanzu haka shugaba Tandja Mamadou na dagewa akan cewar kasar Nijer ba ta da wata matsala ta yunwa, sai dai dan karancin abinci da take fama da shi. Shuagabannin siyasar kasar ta Nijer dake fadar mulki ta Yammai sun sa kafa ne suka yi fatali da matsalolin kasar, ganin cewar su kansu babu wata ribar da zasu samu daga matakan taimakon da ake bayarwa. Wajibi ne a ganawarsa da jami’an siyasar Nijer, sakatare-janar Kofi Annan ya bayyanar musu a fili cewar suna fa da babban alhakin da ya rataya a wuyansu dangane da makomar rayuwar al’umar wannan kasa. Abin takaici ne ganin yadda wasu daga cikin jami’an siyasa da mahukuntan kasar ta Nijer ke ba wa dangi da mukarrabansu kayan taimakon domin sayarwa a kasashe makobta. Kazalika abin Allah waddai ne ganin yadda mahukuntan kasar ta yammacin Afurka suka zura ido akan kungiyoyin taimako daga sassa daban-daban na duniya ba tare da rufa musu baya a matakansu na agaji ba. Bisa ga dukkan alamu dai musunta matsalar yunwar da gwamnatin Nijer ke yi wani yunkuri ne na kare martabarta a idanun duniya. Saboda kasar tayi shekara da shekaru tana samun taimakon raya kasa daga kasashe masu ci gaban masana’antu. Abu mafi alheri shi ne a yi amfani da wadannan kudade wajen raya ayyukan noma da ilimi da kiwon lafiya. Ilimi dai shi ne babban mabudin ci gaba a wannan shiyya. A halin yanzu haka alkaluma sun nuna cewar kimanin kashi 93% na mata a kasar Nijer ba su san bihim ba, wato ba su iya rubutu da karatu ba. Matsawar da ba a shawo kann wannan lamari ba to kuwa da wuya kasar ta yunkura ballantana ta kama wata hanya ta raya makomarta. Sai tare da ilimi ne za a nemo sabbin fasahohi na doma da tattalin ruwa wadanda suke daga cikin muhimman sharuddan hana kasar ta yammacin Afurka sake fadawa cikin wani sabon mawuyacin hali na kaka-nika-yi nan gaba. Domin kuwa ko da yake taimako abu ne da ake madalla da shi, amma dogaro da kai shi ne a’ala ga rayuwar dan-Adam.