1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Kofi Annan a Lebanon

A yau sakataren Majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan zai isa birnin Beirut domin tattauna batun tura sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya zuwa kudancin Lebanon. Kofi Annan zai gana da P/M kasar Fuad Siniora da kakakin Majalisar dokoki Nabih Berri da kuma manyan yan siyasa. Ana sa ran zai matsa kaimi ga shugabanin a game da buƙatar dake akwai ga ƙasar Lebanon ta sanya cikakken tsaro a kan iyakokin ta da ƙasar Syria inda ake kyautata zaton ta nan ne Hizbullah ke fasakwaurin makamai daga Iran. A waje guda kuma shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah yace dakarun Hizbullah ba zasu nuna turjiya ga sojin kiyaye zaman lafiyar na Majalisar ɗinkin duniya ba. Yana mai cewa ko kaɗan basu da matsala da sojojin na UNIFIL matuƙar ba zasu nemi kwance damarar Hizbullah ba. Ziyarar Kofi Annan zuwa ƙasar ta Lebanon ta biyo bayan alkawarin da ƙungiyar tarayyar turai ta yi ne na bayar da gudunmawar sojoji 7,000 waɗanda za su haɗu domin aikin shiga tsakani ta wanzar da zaman lafiya, bayan ɗauki ba daɗi wanda aka shafe tsawon kwanaki 34 ana gwabzawa tsakanin Israila da Hizbullah. Sakataren Majalisar ɗinkin duniyar yace ana fatan tura dakarun sojin nan da mako guda.