ZIYARAR KHARZAI NA AFGANISTAN IZUWA JAMUS. | Siyasa | DW | 30.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIYARAR KHARZAI NA AFGANISTAN IZUWA JAMUS.

WAN NAN HOTON SHUGABA KHARZAI NE TARE DA WANI BABBAN JAMII A NAN JAMUS JIM KADAN BAYAN ISOWAR SA BERLIN.

default

Shugaba Hamid Kharzai na Afganistan ya tabbatar da cewa noman miyagun kwayoyi da wasu bata garin mutane keyi a cikin kasar na daya daga cikin dalilan dake dawo da hannun agogo baya dangane daci gaban kasar ta Fannonin rayuwar bil adama daban daban.

Shugaban na Afganistan yaci gaba da cewa gwamnatin sa a can baya tayi kuskure na kin mayar da hankali wajen yakar mutanen dake noma wadan nan miyagun kwayoyi,to amma a halin yanzu sun gane kuren su,wanda bisa hakan ne a yanzu haka suka dukufa kain da nain wajen daukar matakan shawo kann matsalar.

Bisa wan nan mataki da kasar ke dauka a cewar Hamid Kharzai a yanzu haka jamian tsaro na kasashen Amurka da Biritaniya da kuma Jamus na bawa jamian tsaron kasar horo na musanman dangane da yadda za a iya shawo kann wan nan matsala dake ciwa kasar ta Afganistan tuwo a kwarya.

Koda a yau talata a cewar shugaban sai da jamian tsaron kasar suka kai wani mamaye cibiyoyin da ake gudanar da wan nan mummunar sanaar dake yankin Nangarhar,wanda sakamakon hakan sukayi awon gaba da mutane guda talatin dake da nasaba da yada mummunan aikin,a hannu daya kuma da kwace miyagun kwayoyin masu yawan gaske.

Hamid Kharzai ya fadi hakan ne a yau talata jim kadan kafin tashin sa izuwa tarayyar Jamus don halartar taron wata ginauniya da za a gudanar ta neman kokon bara na sake gina kasar ta Afganistan.

Rahotanni da suka iso mana a yanzu haka sun shaidar da cewa tuni jirgin daya dauko Hamid Kharzai ya sauka a tarayyar ta Jamus domin halartar taron neman tallafin bunkasa aiy