1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Karzai a Jamus

Shugaban kasar Afghanistna Hamid Karzai ya fara wata ziyarar aiki anan Jamus.

Da yake magana da manema labari jim kadan bayan isowarsa birnin Düsseldorf dake yammacin Jamus,Karzai ya yabawa Jamus bisa kokarinta na sake gina kasarsa.

Kasar ta Jamus dai tana da kimanin dakarunta 3,000 karkashin rundunar tsaro ta NATO a kasar ta Afghanistan.

A gobe litinin ne idan Allah ya kai mu shugaba Karzai zai gana da shugabar gwamnati Angela Merkel a birnin Berlin.