1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa hulda tsakanin Saliyo da Najeriya

May 30, 2018

A cigaba da kokarin bunkasa tattalin arziki da hulda tsakanin kasashe a yankin yammacin Afirka, shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya kai wata ziyarar aiki ta wuni daya a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/2yeDY
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari mit sierra-leonischem Präsident Julius Maada Bio
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio a AbujaHoto: DW/U. Musa

Dukkaninsu Biyu dai na zaman tsofaffin janar-janar na soja a kasashensu sannan kuma dukkaninsu sun mulki kasashen nasu karkashin mukin soja ko bayan nan kuma sun yi nasarar darewa a gadon mulki a bisa inuwar jam’iyyar APC ta adawa bayan doguwar gwagwarmaya ta siyasa a kasashensu. 

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari mit sierra-leonischem Präsident Julius Maada Bio
Shugaba Buhari na gaisawa da takwaransa na Saliyo Maada BioHoto: DW/U. Musa

Ziyarar da ke zaman irinta ta farko tun bayan zabensa a cikin wata gwagwarmaya mai zafi a watan Maris din da ya shude dai na da burin kari na hadin kai da kuma kokari na aiki tare da nufin kaiwa ga kara karfafa tattalin arziki na kasashen Biyu. Bayan share kusan mintuna 45 suna tattaunawa da Shugaba Buhari, Shugaba Maada Bio na kasar ta Saliyo dai ya ce sun tattauna abubuwa da dama kama daga tattalin arziki ya zuwa baranar annoba cutar Ebola mai kisa cikin gaggawa da yanzu ake fuskantar ta a kasar Kwango.

Ko bayan taka rawa wajen kare yakin basasa na shekara da shekaru a kasar ta Saliyo dai, Tarrayar Najeriya ta kuma taimaka wajen shawon kan matsalar annoba cutar Ebola mai kisa cikin gagawa da kasar ta Saliyo ta fuskanta. To sai dai kuma a wannan karo kuma a fadar kakakin gwamnatin ta Abuja Mallam Garba Shehu, Maada Bio na neman zuba jari na 'yan kasuwar Tarrayar Najeriyar a cikin harkokin kasuwancin kasarsa ta Saliyo.