Ziyarar jamian binciken Britania a Moscow | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar jamian binciken Britania a Moscow

Jamian binciken Britania dake ziyara a birnin Moscon kasar Rasha ,domin binciken kisan gillan tsohon jamiin leken asiri na Rasha,Alexander Litvinento,zasu gana da babban mai bada shaida Andrei Lugovoi.tsohon jamiin leken asiri Mr lugovoi,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na ITAR-TASS dake rashan cewa,ganawar zata gudana ne a bayyanar jamian gabatar da kara da ofishin babban Alkalin kasar ta Rasha.Shi dai Mr Lugovoi,na daya daga cikin wadanda suka gana da marigayi Litinenko a birnin london ranar daya ga watan nuwamban daya gabata.Litininko dake zama tsohon Conel a hukumar leken asirin Rasha,ya mutu ne aranar 23 ga watan daya gabata,wanda aka dangane da kisan gilla da guba.