Ziyarar jakadun AU zuwa Darfur mako mai zuwa | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar jakadun AU zuwa Darfur mako mai zuwa

A ranar litinin ne idan Allah ya kaimu jakadun AU zasu kai ziyara Khartoum a wani sabon yunkuri na farfado na shirin zaman lafiya a Darfur.

Jakadan musamman na AU Salim Ahmed Salim da shugaba Umar Alpha Konare zasu gana da jamian Sudan da kuma yan tawayen darfur wadanda har yanzu basu rattaba hannu kann yarjejeniyar zaman lafiya na yankin ba.

Ziyarar ta Konare da tawagarsa tazo ne kafin wani taron majalisar tsaro ta kungiyar AU ranar alhamis a Abuja taraiyar Najeriya,inda ake sa ran shugabanin kasashe 15 tare da nufin yanke shawara kan ainihin hanyoyin da MDD zata shiga aiyukan zaman lafiya na Darfur.

A halin da ake ciki kuma wani mai baiwa shugaba Umar al Bashir shawara kuma yace akwai yiwuwar gudanar da taro da yan tawaye a wata mai zuwa a birnin Asmara na kasar Eritrea.

Kanfanin dillancin labaru na Sudan SUNA ya bada rahoton cewa mai baiwa shugaban shawar Mustafa Osman Ismail wanda bada jimawanan ba ya komo daga rangadin kasashen larabawa da turai yana mai baiyana cewa zaa gudanar da taron idan shirye shiryen sun gudana yadda ake bukata,sai dai bai baiyana wadanda zasu halarci taron ba.