Ziyarar Ibrahim Gambari a Nahiyar Asia. | Siyasa | DW | 16.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Ibrahim Gambari a Nahiyar Asia.

Manzon Majalisar ɗinkin duniya Ibrahim Gambari na rangadin ƙasashe shida na yakin Asia domin shawo kan gwamnatin mulkin sojin Myanmar

Ibrahim Gambari da jagorar cigaban dimokradɗiya ta Burma Aung San Suu Kyi

Ibrahim Gambari da jagorar cigaban dimokradɗiya ta Burma Aung San Suu Kyi

Jakadan Majalisar ɗinkin duniyar Ibrahim Gambari wanda ya fara yada zango a ƙasar Malaysia inda daga nan zai wuce zuwa ƙasashen Indonesia da India da China da kuma Japan ya jaddada buƙatar ƙasashen na Asia waɗanda ke maƙwabtaka da Myanmar su haɗa kai wajen jawo hankali mahukuntan gwamnatin mulkin ta Myanmar su dakatar da cin zarafi da azabtarwar da suke wa mutanen da suka tsare a sakamakon zanga zangar lumana da suka gudanar ta neman cigaban mulkin dimokraɗiya.

Ibrahim Gambari ya baiyana matuƙar damuwa da cigaba da kame da kuma amfani da ƙarfi da sojoji ke yi a kan jamaá fararen hula, yace cigaba da tsare shugabanin ɗaliban addinin Buddah da azabtar da su da gwamnatin ke yi babban abin takaici ne, ya kuma saba da muámala ta fahimtar juna tsakanin Majalisar ɗinkin duniya da Myanmar. Yace Wajibi ne a dakatar da wannan cin zarafi nan take. Bugu da ƙari Ibrahim Gambari ya kuma yi kara ga gwamnatin ta Myanmar ta sako dukkan fursunonin siyasa da take tsare da su waɗanda suka haɗa da mutanen da aka kame a lokacin zanga zangar lumana da ta gudana a baya bayan.

A cikin watan Nuwamba mai zuwa Ibrahim Gambari zai sake komawa ƙasar ta Myanmar domin sake tattaunawa da shugabanin mulkin sojin kan buƙatar sako fursunoni kimanin dubu daya da gwamnatin ke tsare da su da kuma buƙatar warware rikicin ƙasar ta hanyar lumana.

Shima shugaban Amurka George W Bush ya yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara matsa ƙaimi a kan gwamnatin mulkin sojin ta Myanmar domin tilasta musu rungumar tafarkin dimokraɗiya da wanzuwar lumana. Bush yace abin da ake buƙata shine haɗin kan gamaiyar ƙasa da ƙasa ta hanyar mayar da shugabanin mulkin sojin saniyar ware a dukkan alámura da kuma nusar da su cewa ko kusa ba zaá lamunta da irin cin zarafin da suke wa jamaá fararen hula ba. Bush ya kuma baiyana aniyar bada tallafin kuɗi ga masu fafutukar cigaban dimokraɗiyar ta Myanmar.

A hannu guda kuma a irin matakan matsin lamba ga mahukuntan gwamnatin mulkin sojin, ƙasar japan ta soke gudunmawar jin kai na maƙudan kuɗaɗe ga gwamnatin Myanmar domin baiyana ɓacin ran ta ga kisan wani ɗan jarida Kenji Nagai ɗan ƙasar japan a sakamakon dirar mikiyar da sojoji suka yi a lokacin zanga zangar.

Babban sakataren gwamnati a birnin Tokyo yace gwamnatin ta soke tallafin da ta yi niyyar baiwa Myanmar na tsabar kuɗi dala miliyan 552. Ita ma ƙungiyar tarayyar turai a taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar ta amince da wasu jerin takunkumi a kan gwamnatin Myanmar wanda ya haɗa da haramta shigar da kayayyakin ta zuwa nahiyar turai, Ko kuma sayar mata da wasu kayayyakin buƙatu.

Rahotanni dai daga ƙasar ta Myanmar na cewa gwamnatin mulkin sojin ta kama karya, ta yi watsi da haɗin kan gamaiyar ƙasa da ƙasa da kuma dukkan wani mataki da zasu ɗauka a kan ta.

A watan Satumban da ya gabata ƙasar Myanmar ta fuskanci zanga zangar adawa mafi girma inda mutane fiye da dubu ɗari ɗaya waɗanda suka haɗa da ɗaliban addinin Buddah suka fito tituna domin adawar su da gwamnatin. Mahukuntan mulkin sojin sun yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa zangar zangar wanda ya yi sanadiyar mutuwar a ƙalla mutane 13 tare kuma da kame wasu mutanen fiye da 2,000 waɗanda gwamnatin ta tsare a gidajen yari.