Ziyarar Hillary Clinton a Liberiya | Siyasa | DW | 14.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Hillary Clinton a Liberiya

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Hillary Clinton na cigaba da ziyara aikin kwanaki 11 a nahiyar Afirka.

default

Ziyayar Hillary Clinton a Afrika

A cigaban ziyarar ta a ƙasashen Afrika, Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Hillary clinton ta isa Laberiya, inda ta yabawa shugabar ƙasar Ellen Johnson Searlef ƙoƙarin da take, na daidaita ƙasar bayan yaƙin sama da shekaru goma, da ta yi fama da shi.

Dubban mutane sukayi dafifi akan titinan Monroviya babban birnin ƙasar Laberiya,domin nuna murna ga ziyarar Clinton a wannan ƙasa da Amurka ta ƙirƙiro a farkon ƙarni na 19 domin tsugunar da bayin da ta yanta a wancan lokaci.

Yayin jawabinta, Clinton ta yabawa ƙasar ta na mai cewa: zamu ci gaba da bada goyon baya a gwamnatin Laberiya domin samar da zaman lafiya da ingantacen shirin raya ƙasa , ta kuma yabawa Shugabar ƙasar a matsayinta na macen farko da ke shugabanci a Afrika tana mai nunin cewa mata suna da rawar da zasu iya takawa wajan cigaban ƙasa.

Ƙasashen duniya dai na maida hankalinsu ne kan shari´ ar da ake wa tsohun madugun yan tawaye, kuma tsohun shugaban ƙasar Laberiya Charles Tailor ,a kotun hukunta masu leffukan yaƙi dake birnin Hague bisa lefuffukan da suka haɗa da kisan mutane, fyaɗe, saka yara aikin soja, da kuma cin naman mutane.

A baya dai ,hukumar binciken gaskiya da daidaita tsakani ta zargi shugabar ƙasar da lefin taimakawa Charles Tailor a lefuffukan da ya aikata, zargin da ita kuma ta musanta, tace a baya dai tasha ganawa da shi harma ta taɓa bashi taimakon kuɗi, amma bata taɓa shiga Ƙungiyarsa ta National Patriotic Front ba, abinda da kuma ya jawo mata baƙin jini tare da kiranye-kirenyen ta sauka daga mulki.

Bayan Laberiya, a yau ne dai Hillary Clinton zata zarce tsibirin Cape Verd a zangon ta na ƙarshe a ziyarar da ta kawo Afrika.

Mawallafi: Ibrahim Mohamed.

Edita: Yahouza Sadissou