Ziyarar Guido Westerwelle a Afirka | Siyasa | DW | 21.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Guido Westerwelle a Afirka

Ministan harakokin wajen Jamus ya halarci taron Ƙungiyar Gamayyar Afirka a birnin Kampala na Yuganda

default

Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle

A wannan Larabar,ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya fara ziyara karo na biyu a nahiyar Afirka inda zai halarci taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka a birnin Kampala na ƙasar Yuganda.

Taron na Ƙungiyar AU na wakana kawanki kaɗan bayan da birnin Kampaka ya yi fama da hare-haren ta´addanci daga Ƙungiyar Al-Shebab mai tsatsauran ra´ayin addinin Islama  a ƙasar Somaliya,wanda su ka yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 80.

Guido Westerwelle zai amfani da wannan dama, domin tattanawa da takwarosinsa na ƙasashen Afirka game da hanyoyin yaƙi da ta´addanci. A shekaru baya, abin mamaki ne wani ministan harakokin wajen Jamus ya halarci taron ƙasashen Afirka, amma yanzu akalar diplomasiyar duniya ta cenza, kuma kamar yadda hausawan ke faɗi ,idan kiɗi ya cenza rawa ma ta kan cenzawa.Masana harakokin diplomasiya a nan Jamus, sun lura da cewar a halin da ake ciki fadar mulkin birnin Berlin na ƙara sa ido ga al´ammuran da ke wakana a Afirka saɓanin sherkarun baya, wannan kuma ba zai rasa nasaba ba, da zawarcin Afirka a yunƙurin Jamus na samun kujera dindindin na komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma  bunƙasa saye da sayarwa, kamar yadda Andreas Mehler shugaban cibiyar nazarin siyasa ta birnin Hambourg ya yi bayani:

"Mun lunra da cewar akwai kishi tsakanin manyan ƙasashen duniya ta fannin samun makamashi daga Afirka.ta la´akari da yadda ƙasar China ta kutsa cikin kasuwanin ma´adanai a Afirka, ya sa wannan nahiya ta kara samun farin jini.

Ba´ada bayan wannan batu, ko shakka babu Guido Westerwelle zai gana da takwarorinsa na Afirka game da sha´anin tsaro , musamman bayan ta´adin da ya gudana a birnin Kampala ,wanda kuma ya jefa sauran ƙasashen yankin cikin zaman ɗar-ɗar kamar yadda Mohamed Maundi jikadan Tanzaniya a  Ƙungiyar Tarayya Afirka ya bayyana:

"Lalle Somaliya ce cibiyar wannan rikici, to amma  a zahiri ba shi da iyaka.Idan ba  haɗa ƙarfi da ƙarfe a ka magance shi ba, to zai ɓulla wasu ƙasashe kmar Yuganda Keniya.saboda haka yauni ya rataya kan Afrika baki ɗaya ta magance rikicin Somaliya".

A halin yanzu Afrika na da sojoji dubu shidda a Somaliya mafi yawan su daga ƙasar Yuganda,kuma bakin gwargwado sun taka rawar gani domin sun yi nasarar kare fadar shugaban ƙasa da kuma wasu manyan titina na birnin Mogadiscio.Shugaban ƙasar Yuganda Yuweri Museveni bayan harin Kampala, ya yi kira da a ƙara yawan sojojin Afiorka a Somaliya, har zuwa dubu 20.Idan wannan kira ya samu shiga cilas Afirka na buƙatar kuɗaɗe masu yawa daga ƙetare, saboda haka wannan batu shima zai kasance sahun gaba a ajendar ganawa tsakanin ministocin harakokin wajen Afirka da Guido Westerwelle.

 Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu