1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Gates a Iraƙi

Halimatu AbbasDecember 5, 2007
https://p.dw.com/p/CXZA

Sakataren tsaron Amirka Robert Gates ya kai wata ziyara ta ba zata a ƙasar Iraki domin shawo kan shugabannin kasar ga yin sulhu da ya ke an samu raguwar tashe tashen hankula.Zai gana da shugaba Jalal Talabani da prime minista Nuri Almaliki domin shawarta ko shin gwamnatin ƙasar da yan shia ke jagoranta zata iya sasantawa tare da yan sunni tu kuma zartar da dokar samar da zaman lafiya tsakaninsu.Gates zai kuma gana da shugabannin dakarun Amurka don tattauna yanda za a inganta aikin tsaro.Gates ya kai wannan ziyara ne wasu yan kwanaki kaɗan bayan shugaba Bush da Maliki sun cimma matsaya akan dawammar da dakarun Amurka a Iraki zuwa shekara ta 2009.A wata sabuwar kuma yan ta’adda da suka sace wasu yan ƙasar Birtaniya su biyar tun a watan Mayun da ya gabata sun fid da wani video da ke barazanar yi wa ɗaya daga cikinsu kisa, in har Birtaniya ba ta janye dakarunta daga ƙasar ba.