Ziyarar Gates a Bagadaza | Labarai | DW | 19.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Gates a Bagadaza

Sakataren tsaro na Amurka Robert Gates ya gana da manyan commandojin rundunar sojin Amurka dake Iraki ,da saukarsa yau a kasar,yini guda bayan boma bomai sun hallaka rayukan mutane kusan 200 biyu a kasar,batu dake bayyana gazawar Amurka wajen shawo kann matsalolin tsaro a wannan kasa.

A wannan ziyara tasa dake zama na ukun irinsa a Irakin,bayan hawan karagar mulki,Mr Gates ya gana da manyan jamian tsaron Amurkan a sansaninsu ne dake kusa da garin Fallujah,a wannan rangadi nasa na bazata a yankin gabas ta tsakiya.Jim kadan da isarsa Irakin ayau ne,sojin Amurkan suka sanar da mutuwan karin jamiansu guda 3,wanda ya kawo ga adadin dakarun Amurkan 3,313 kenan suka rasa rayukansu a hukumance,tun bayan afkawa kasar da karfin soji.A Bagadaza da kewaye dai Yan siyasa da alummomin kasar na cigaba da Allah wadan