Ziyarar Gates a Afganistan
September 2, 2010Sakataran tsaro na Amirka Robert Gates ya fara wata ziyarar aiki ta ba-zata a yau a Afganistan bayan wadda ya kammala a ƙasar Iraƙi, inda ya bayyana kawo ƙarshen kai hare-haren dakarun AmIrka a yaƙin da gwamnatin ƙasar ta ke yi da 'yan ƙungiyar Taliban. Ziyarar ta Gates wacce ta zo a daidai lokacin da dakarun Amirkan da ke da yawan kashi biyu cikin ukku na dakarun ƙasashen duniya kimanin dubu 150 a Afganistan na yin bita akan irin mumunar asarar rayukan jama'a da suka samu a tsawon watannin tara na yaƙin da suka gwabza da ƙungiyar Taliban. An shirya dai sakataren tsaron na Amirka zai gana da Shugaba Hamid Karzai a birnin Kabul da kuma babban kwamandan dakarun ƙawance na ƙasa da ƙasa Janar David Petraeus.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas