Ziyarar Fraministan Rasha a Jamus | Labarai | DW | 26.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Fraministan Rasha a Jamus

Yau Fraministan Rasha,Vladimir Putin ke ganawa da Angela Merkel a Berlin babban birnin Jamus.

default

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da Framinista Vladimir Putin na Rasha

Fraministan Rasha, Vladimir Putin ya iso birnin Berlin na Jamus inda zai shiga tattaunawa tare da Shugabar gwamnati, Angela Merkel a yau ɗin nan. Yayin wannan ziyara tasa Putin zai yi jawabi ga shugabannin kamfanonin Jamus a birnin na Berlin. Tun da farko Merkel ta soki Rasha bisa manufatrta ta kare muradunta na ciniki da ka iya kawo cikas ga cinikin da Jamus ke yi da ƙasashen ƙetare. Ta ce manufofin Putin sun saɓa wa ƙudurinsa na samar da walwalar kasuwanci kama daga ƙasar Portugal zuwa Rasha. A yayin ganawar da za su yi a yau ɗin nan ana sa rai cewa Putin da Merkel za su tattauna akan raɗi- raɗin cewa babban kamfanin makamashin Jamus, E-on na shirin sayar da hannayen jarinsa ga kamfanin gas na Rasha wato Gazprom kamar yadda wata jaridar Rasha ta tsegunta.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu