Ziyarar Fischer A Asiya | Siyasa | DW | 11.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Fischer A Asiya

Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya kammala ziyararsa ga kasashen Asiya inda ya gane wa idanuwansa barnar da masifar tsunami tayi wa kasashen yankin

Fischer A Thailand

Fischer A Thailand

An dai saurara daga bakin Jan Eil Mosand mai jan akalar matakan taimako na MDD a kasar Thailand yana mai kiran dakatar da ‚yan siyasa kai ziyara wuraren da bala’in tsunami ya rutsa da su. Dalilinsa game da wannan kira kuwa, kamar yadda ya ba da misali shi ne, ganin yadda aka toshe filin saukar jiragen saman Banda Aceh tsawon sa’o’i masu yawa sakamakon ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell a wannan yanki. An fuskanci irin wannan matsala a sauran yankunan da bala’in ya shafa. Ba shakka hakan ba abu ne da ya dace ba, kuma lamari ne da za a iya kauce masa idan an shirya kome a bisa nagartaccen tsari. Amma zai zama ragon azanci ko kuma babban kuskure a ce za a dakatar da jami’an siyasa kai ziyarar ganin ido a wuraren da bala’i tsunami ya rutsa da su a kudancin Asiya. Misali dai ziyarar da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya kai baya-bayan nan zuwa yankunan Phuket da Khao Lak, wacce ke da nufin girmama Jamusawan da bala’in ya rutsa da su da kuma taya danginsu juyayi. A can Indonesiya da Sri Lanka kuwa, ministan harkokin wajen na Jamus, a baya ga zumuncin da ya nuna ga wadanda bala’in ya rutsa da su, ya kuma share hanyar ci gaba da taimakon da ake bayarwa a siyasance, lamarin da ba makawa yake da muhimmanci matuka ainun. Ba za a iya gabatar da taimakon jinkai a wani yankin da za a kebe shi daga manufofi na siyasa ba. A dukkan kasashen Indonesiya da Sri Lanka masifar ta tsunami ta rutsa ne da yankunan kasashen biyu da ake fama da yakin basasa a cikinsu. Ta la’akari da haka duk wani mataki na taimakon sake ginawar da za a dauka wajibi ne ya tafi kafada-da-kafada da manufofin neman bakin zaren warware wadannan rikice-rikice a siyasance. Mai yiwuwa da zarar kungiyoyin taimakon na kasa da kasa sun fara jin rugugin albarusai a gwabzawar da ake yi tsakanin sojan gwamnatin Indonesiya da dakarun ‚yan tawaye a Aceh, sannan ne zasu farga cewar ba za a iya gabatar da taimako a karkashin irin wannan yanayi ba. An lura da haka a kasar Ruwanda a misalin shekaru 10 da suka wuce, inda jami’an taimakon jinkan na kasa da kasa suka kasa tabuka kome domin dakatar da rikici tsakanin ‚yan Hutu da ‚yan Tutsi. Wadannan kungiyoyi ba su da ta cewa a al’amuran siyasa bisa sabanin wani minista na harkokin waje. Wannan damar ce kuma Fischer yayi amfani da ita a ziyarar da ya kai Indonesiya, inda a baya ga gaisuwar ta’aziyya ya kuma janyo hankalin shugaban kasar Susilo Bambang Yudhoyono zuwa ga muhimmancin dake akwai wajen sanya matakan taimakon jinkan da ake bayarwa su tafi kafada-da-kafada da manufofin neman bakin zaren warware rikicin lardin Aceh a siyasance.