1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Firimiyan kasar Sin a Afrika

Hauwa Abubakar AjejeJune 21, 2006

ana ganin wannan ziyara,tana da alaka da samarda makamashi ga kasar Sin,da kuma inganta manufofinta na ketare

https://p.dw.com/p/Btzf
Firimiya Wen Jiabao
Firimiya Wen JiabaoHoto: AP

Kafofin yada labarai na gwamnatin Sin suna ganin wannan ziyara ta Wen Jiabao,wata alama ce cewa,kasar Sin tana matsayin daya daga cikin manyan kasashen duniya wadda bata neman ci da gumin wasu kasashe domin ci gaban tattalin arziki da siyasarta,wadda jamian diplomaiya na kasar suke cewa,kasar Sin tana mika taimako ba tare da ta gindaya sharudda ga kasashe matalauta ba.

Masu suka ga kasar ta Sin kuwa cewa sukayi,harkokin diplomasiya da kasar ta bullo da su kwanan nan musamman ziyarar Wen Jiabao,sun nuna irin kwadayin makamashi da take da shine,wanda ya kai ta ga kulla cinikin mai da albarkatu tsakaninta da kasashe da a cewarsu basu dace ba kamar,Sudan da Zimbabwe

Amma gwamnatin kasar ta kare kanta daga wannan zargi,tana mai cewa,bai dace ba a ce dangantaka da yanzu ke kulluwa tsakanin sin da kasashen Afrika ya dogara ne akan mai kadai,inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar He Yafei ya baiyanawa manema labarai cewa,manufar wannan dangantaka itace ta cude ni in cude ka,wanda yace musaman saboda ci gaban kasashen Afrika.

Hakazalika wata jaridar kasar sin ta baiyana cewa,kasar ta Sin bata bada wasu sharudda ko kaidoji na canje canjen siyasa ko manufofin tattalin arzikin ga kasashen Afrika,wajen basu rance,haka kuma tana kara karfafa masu gwiwa wajen saka jari domin inganta tattalin arzikinsu.

Sai dai wani jamiin diplomasiya na kasashen yamma yace,wannan tsari na kasar Sin yana a matsayin kunyata kasar Amurka da kasashen yamma ne,musamman dangane da manufofinsu na ketare.

Masu bincike sun nuna cewa,ziyarar Wen ya nuna sauya akalar dangantaka ko kuma bada fifiko na gwamnatin Sin daga dangantaka tsakaninta da kasashe da suka ci gaba,zuwa kasashen Afrika,ba kamar tsohon shugaba Jiang zemin da yafi bada fifiko kan dangantaka da Amurka ba.

A matsayin wani bangare na samarda hadin kai da kasashe masu tasowa da kuma samarda makamashi,kasar Sin tana baiwa kasashen Afrika taimako ta fannonin tattalin arziki,da basusuka da babu ruwa cikinsu haka zalika kanfanoni na Sin suna gina hanyoyi,da asibitoci,filayen wasanni da hanyoin ruwa,wanda yanzu haka kanfanonin Sin suna gudanar da aiyuka kusan 900 a nahiyar Afrika.

Albarkatun mai dai su ake ganin suke karfafa wannan dangataka ta sin da Afrika,wanda yanzu haka gwamnatin sin ta kashe biliyoyin daloli,wajen samun ikon hako mai a Najeria,Sudan da Angola.

Ta kuma sanya hannu akan yarjeniyoyi na tabo mai a kasashen Afrika da dama,kama daga jamhuriyar demokradiyar Kongo zuwa kasar Habasha.

Kasar Sin tana samun kashi 25 cikin dari na albarkatun mai daga nahaiyar ta Afrika,wadda kuma take shirin karawa akai.

Kasar Angola ce ke kan gaba,wajen baiwa Sin mai,inda a bara tayi cinikin mai na kusan dala biliyan 7,a nata bangare kuma kasar Sin ta bada rancen dala biliyan 3 domin farfado da ababen more rayuwa da suka lalace a lokacin yakin basasa na kasar.

Kasashe kuma kamar su jamhuriyar demokradiyar kongo da Afrika ta kudu wadanda basu da albarkatun mai,wanda kuma suke kan ajandar ziyarar Wen Jiabao,suna da albarkatun tama da karafa,wanda kasar Sin din take bukata.