1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar diflomasiyya a zirin Gaza

June 13, 2010

Ƙungiyar Larabawa ta ce dole ne Isra'ila ta cire ƙawanyar da take yiwa zirin Gaza

https://p.dw.com/p/NprZ
Hoto: AP

Babban sakataren haɗaɗɗiyar ƙungiyar Larabawa Amr Musa, ya gana da shugabannin ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas dake da iko a zirin Gaza, inda ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga al'ummar yankin. Alokacin wannan ziyarar, wadda ita ce irin ta na farko tun bayan da Isra'ila ta yiwa yankin ƙawanya shekaru ukkun da suka gabata dai, Malam Amr Musa ya buƙaci Isra'ila ta cire shingen da take sanyawa yankin ba tare da wani ɓata lokaci ba:

" Ƙawanya : Wannan ƙawanyar da dukkannin mu ke tsaye domin tunƙarar ta, dole ne a karya ta kuma a ire ta. Kuma shawarar da ƙungiyar Larabawa ta yanke a bayyana take game da karya lagon ƙawanyar, da ɗage ta, da kuma rashin mutunta ƙawanyar"

Wannan ziyarar da shugaban ƙungiyar ƙasashen larabawa yakai zirin na Gaza dai, ita ce alama ta baya bayannan dake nuna sake ɗinke sha'anin diflomasiyya da ƙungiyar Hamas, biyo bayan harin zubda jinin da Isra'ila ta kai akan wani jirgin agaji ga Falasɗinawa.

A halin da ake ciki kuma Isra'ila na ƙara fuskantar wariya bayan harin na ranar 31 ga watan Mayu, inda ba zato ba tsammani ministan kula da harkokin tsaron Isra'ila Ehud Barak ya soke ziyarar da ada zai kai birnin Paris na ƙasar Faransa.

Ofishin Ehud Barak dai ya sanar da cewar, ya soke tafiyar ce a dai dai lokacin da hukumomin Isra'ila suka ƙafa kwamitin binciken harin. Sanarwar ta ƙaryata zargin cewar soke tafiyar na da nasaba da ƙoƙarin da wasu ƙungiyoyin nuna goyon bayan Falasɗinawa ke yi na neman a cafke shi.

Mawallafi : Saleh Umar saleh

Edita : Ahmad Tijjani Lawal