Ziyarar da shugaban tarayyar Jamus Johannes Rau ya kai tarayyar Nijeriya. | Siyasa | DW | 19.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar da shugaban tarayyar Jamus Johannes Rau ya kai tarayyar Nijeriya.

Shubaba Rau yana karbar furannin maraba da sauka Nijeriya.

Shubaba Rau yana karbar furannin maraba da sauka Nijeriya.

Alal hakika shugaban tarayyar Jamus Johannes Rau ya so kaiwa birnin Kano ziyara a jiya alhamis. Tun a ranar laraba wata guguwa hade da yashin hamada ta yi ta kadawa a ilahirin jihar ta Kano. Kashe-gari da safe bayan da ta lafa, an ba shugaban da ayarinsa tabbacin cewa suna iya kai wannan ziyara. To amma bayan isar su filin jirgin sama sai aka samu wata sanarwa ta gaggawa, wadda ke cewa ba zasu iya sauka a filin jirgin saman Kano ba saboda lalacewar wata na´ura dake taimakawa saukar jirgin sama. A saboda haka a dole aka soke gudanar da wata tattaunawa mai muhimmanci tsakanin Rau da gwamanan Kano da kuma Sarkin Kano. Kano dai tana matsayin wata cibiyar addinin musulunci kuma tana cikin jihohi 12 na arewacin Nijeriya da ke amfanin da dokokin shari´ar musulunci. Rau kuwa na nuna damuwa ga wannan ci-gaba da aka samu kamar yadda ya nunar a ziyarar da ya kaiwa tarayyar Nijeriya.

Rau ya ce: "Dole mu yi takatsantsan game da kafa dokoki. Domin harka ce mai sarkakkiyar gaske. Ka da mu bari hakan ya zama wata hujja ta barkewar rikicin siyasa ko na addini."

Shi kuwa a nasa bangaren shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeriya cewa yayi ya zuwa yanzu ba´a taba zartas da hukuncin jifa akan wani a Nijeriya ba, kuma ba za´a ´taba yin haka ba muddin yana kan karagar mulkin wannan kasa. Sakatariyar kasa a ma´aikatar raya kasashe masu tasowa ta Jamus Uschi Eid ta bayyana shugaba Obasanjo da cewar shugaba ne da aka saka masa dogon buri, sannan ta kara da cewa:

"Shugaba Obasanjo na taka muhimmiyar rawa a sauye-sauyen da ake aiwatarwa a nahiyar Afirka. Duk wanda ya zo nan zai ga cewar da akwai matsaloli da dama da shugaban yake fuskanta dangane da aiwatar da wadannan sauye-sauye a cikin gida."

Ko da yake shugaba Obasanjo ya kuduri aniyar yaki da cin hanci da karbar rashawa tare da kafa mulkin demukiradiyya mai dorewa a Nijeriya, amma cimma wannan burin abu ne mai wuyar gaske, musamman a wannan kasa mai yawan al´uma kimanin miliyan 130 masu bin addinai da kuma al´adu daban-daban. Ga kuma bambamce-bambamcen dokoki a cikin jihohi 36 dake tarayyar ta Nijeriya. A ma halin da ake ciki wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na korafin cewa maimakon mulkin demukiradiyyar ya kawo ci-gaba sai kara tsundumar da kasar cikin wani hali na rashin sanin tabbas ya ke yi. To amma duk da haka wasu daga cikin kungiyoyin sun ce suna gudanar da aikinsu ba da wata tsangwama daga hukuma ba. Saboda haka tarayyar Jamus zata ci-gaba da taikawa Nijeriya a kokarinta na kafa sahihiyar demukiradiyya.

 • Kwanan wata 19.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlC
 • Kwanan wata 19.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlC