Ziyarar CR a Biritaniya ta fuskanci adawa | Labarai | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar CR a Biritaniya ta fuskanci adawa

Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR tace kifar da mulkin shugaba Saddam Hussain na Iraqi da dakarun sojin Amurka dana kawance suka yi abu ne daya dace.

CR wacce ta fadi hakan a dazu dazun nan a taron manema labarai data gudanar a mahaifar takwaranta na Biritaniya Mr Jack Straw, taci gaba da cewa a kwana a tashi mulkin dimokradiyya zai samu gindin zama a kasar ta Iraqi.

Ziyarar dai ta Rice a mahaifar ta Jack Straw ta fuskanci adawa daga mutanen garin na Blackburn, gari dake da kashi 20 na mabiya addinin musulunci a cikin sa.

Bayanai dai sun nunar da cewa mutanen da yawan su ya tasamma a kalla dari biyu sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da wannan ziyara.

Bugu da kari masu zanga zangar sun kuma bukaci shugabannin biyu dasu gaggauta janye sojojin su daga kasashen Iraq da kuma Afghanistan.