1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Condoleezza Rice a gabas ta tsakiya

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7S

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta fara ziyarar kasashen gabas ta tsakiya domin neman goyon bayan kasashen larabawa dake dasawa da Amurka don daukar kwakwaran mataki akan kasar Iran kama daga batun Nukiliya ya zuwa yan gwagwarmayar jihadi masu tsatsauran raáyi a yankin. A wata hira da ta yi da yan jaridu na kasashen larabawa, Condoleezza Rice ta gargadi Iran ta kiyayi kokarin tallafawa Hamas domin yin hakan zai kara jefa Iran din cikin hali na tsaka mai wuya. Batun karbar ragamar Iko da Hamas ta yi a harkokin siyasar Palasdinu shi ne jigon abin da zata tattauna da mahukunta a yayin ziyarar ta zuwa kasashen Masar da Saudi Arabia da kasar hadaddiyar daular larabawa. Ana sa ran Condoleezza Rice zata bukaci kasashen na larabawa su yanke duk´kan wata hulda da Hamas har sai ta yi watsi da akidar tarzoma ta kuma amince da wanzuwar kasar Israila.