Ziyarar Condoleeza Rice a birnin Bagadaza | Labarai | DW | 17.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Condoleeza Rice a birnin Bagadaza

Sakariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta fadaw shugabannin kasar Iraki cewa ,suyi amfani da damar da suka samu na tsagaitawar tashe tashen hankula wajen sasanta kann kasar,domin Amurka ta kusan bayyana rashin hakurinta kann haka.Rice tayi wannan furuci ne ziyarar bazata data kai Bagadaza ayau,inda tun da farko ta yabawa kokarin dakarun Amurka dana Irakin dangane da samun nasara kann mayakan sakai.Kafin barinta birnin Bagadazan Condoleeza Rice ta gana da prime minista Nuri al-Maliki da shugaba Jalal al-Talabani,kafin ta bayyanawa manema labaru cewa....

Mun sha nazarin tsarin tsaro a Bagadaza,da kuma hanyar da Amurka zata iya taimakawa da goyon bayanta.Annan zan iya bayyana cewa muna matukar farin ciki da shugabancin prime minista Nuri almaliki da ayarin gwamnatinsa.