1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Chirac a Saudi Arabia

Chirac

Shugaba Jacques Chirac na kasar Faransa a ziyara dayakeyi a Saudi Arabia,yayi kira dangane da hakuri da juriya da kuma darajawa martabar addini,dangane da yayata zanen batanci na Annabi Mohammad Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi,a watan daya gabata,batu daya harzuka alummar musulmi a sassa daban daban na duniya.

Wannan jawabi na shugaban na faransa wa majalisar shawarwari na saudi Arabia ,yini guda bayan kira da mataimakin shugaban Alqaeda yayi wa musulmi nayin watsi da kasashen da aka yayata wadannan hotuna na batanci,wanda ya hadar da Faransa.Shugaba Chirac yace da irin cigaba da aka samu a duniya,babu abunda zaayi a boye,domin haka dole ne a hada kai baki daya domin kawo zaman lafiya a duniya.Yace dole ne a guji dukkan wani abu dazai iya harzuka wani,ko wata alumma,inda ya jaddada muhimmancin mahawara da juna idan buta ta taso.

Ayayin wannan ziyara tasa ta yini uku dake karewa gobe litinin,shugaban na faransa zai nemi bawa kamfanonin kasarsa kwangila a saudi Arabiya,kasar da Amurka da Britania suka samu gindin zama.

 • Kwanan wata 05.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7d
 • Kwanan wata 05.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7d