Ziyarar Bush a yankin gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 16.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Bush a yankin gabas ta tsakiya

Bush ya gama ziyara ba tare da cimma manufa ba a yankin gabas ta tsakiya

default

George W. Bush da sarki Abdallah

Shugaban na Amurka wanda yasha nunar dacewar ɗaya daga cikin manufofin gwamnatin sa na ketare shine tabbatar da zaman lafiya tsakanin Izraela da Palastinu,ya ziyarci wannan yankin ba tare da yin wani tasiri daga halin da suke ciki ba.Sai dai yayi alkawari a karshen ziyarar tas nacewar,zai cigaba da taka rawa wajen ganin cewar an cimmam sulhu mai ɗorewa tsakanin Izraela da yankin na Palasdinawa, kafin karshen wa'adin sa na mulki.

To sai dai waɗannan kalamai na Bush sun zame tamkar wakace daya saba yi inji Mataimakin Direktan cibiyar nazarin harkokin ƙasa da ƙasa dake Masar Dr Mohammed.


"Yasha mayar da hankali kan yankin gabas ta tsakiya a manufofin sa ketare,amma a aikace babu wani tasiri da manufofin nasa suke yi ,kuma kawo yanzu babu alamun akwai ranar da za a kai ga cin musu,ziyarar dayakai wannan yankin bashi da amafani ,domin yaje rangadi ne a inda ake kyamar sa"


Shugaba Bush ya yi amfani da wannan rangadin aiki daya kai,wajen kira ga kasashen Syria da Iran dasu tsame hannuwan su daga cikin harkokin siyasar ƙasar Libanon, wanda inji shi hakan ne zai bata damar zaɓen shugaban ƙasa.


To sai dai muhimmin batu da Bush ya mayar da hankali akai a wannan rangadi nasa shine bukatar goyon bayan ƙasashen Larabawan wajen mayar da Iran saniyar ware,inda ya bayyana ta da kasancewa babbar barazana ce a gare su sakamakon shirin nuclearn ta.


Duk dacewar kasashen Larabawan na shakku dangane da yadda Iran ke dada samun karfi a yankin,a fili take basa muradin ganin Amurka tayi amfani da karfin soji a kan Tehran.


Ministan harkokin wajen Saudiyya Saud al-Faisal yace Iran makwabciyar su ce,kuma tana da matukar tasiri a wannan yaanki nasu,don haka basu da wani dalili na nuna adawa da ita.Sai dai ya jaddad bukatar ƙasar ta amince da dukkannin bukatun ƙasashen duniya dangane yin ayyuka halaltattu.


A ziyarar sa zuwa masarautun Bahrain da Haɗaɗdiyyar daular Larabawa da Kuwaiti da Saudiyya da Masar dai,shugaban na Amurka ya nemi haɗin kan su nan ma wajen cimma sansanta Izraela da yankin Palastinawa.


Kafar sa ta farko a wannan rangadi nasa a makon daya gabata dai shine Izraela,sa'annan gabar yamma da kogin Jordan,inda yace yana muradin ganin sun rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kafin wa'adin mulkin sa a watan janairun 2009,batu da Dr Mohamme yace abu ne mawuyaci..

"

A irin takun sakar sa ,kuma bisa laakari da yan watanni da suka rage masa akan karagar mulki,abune mawuyaci a cimma wadannan manufofi nasa daya aiyyana"