1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Bush a kudancin Amurka

March 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuPw

Shugaban Amurka George W Bush wanda ke rangadi a kasar Uruguay a cigaba da ziyarar yankin kudancin Amurka, ya yi watsi da sukan da shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez yake masa wanda shi ma ke makamanciyar ziyarar ta akasin Bush. A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar tare da shugaban Uruguay Tabare Vazquez, Bush yace kafa masanaántu shi ne jigon yaki da talauci a kudancin Amurka. A nasa bangaren Chavez a ziyarar da ya kai zuwa Bolivia, ya bukaci dubban jamaár wadanda ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da cewa sai su yi zabi tsakanin jari hujja da kuma mulki na alúma. A ranar lahadin nan Bush zai nufi Colombia inda dubban dalibai wadanda ke adawa da ziyarar sa ke ta dauki ba dadi da yan sanda gabanin ziyarar ta Bush. Ana sa ran shugaban kasar Colombia Alvaro Uribe zai maida hankali ga bukatar Amurka ta samar da kudade na dawainiyar yaki da safarar kwayoyi.